Labarai
Sojojin Sudan Sun Kace Birnin El-Obeid Daga Hannun RSF
Sojojin Sudan sun ce sun kawo ƙarshen iko da birnin el-Obeid na yankin kudancin ƙasar na kusan shekaru biyu da dakarun RSF suka yi.
Wannan nasara na zuwa ne ‘ƴan sa’o’i bayan da RSF ta rattaɓa hannu kan yarjejeniyar siyasa a Nairobi da ke ƙasar Kenya na kafa gwamnatin aware a yankunan da ke ƙarƙshin ikonta.
Tun dai shekarar 2023 ne rundunar RSF da sojojin Sudan ke fafatawa, inda dubban fararen hula ke mutuwa sannan da dama na barin gidajensu.
Rikicin dai ya raba ƙasar ɓangarori biyu, inda sojoji ke iko da arewa da gabashi, yayin da su kuma RSF ke iko da mafi yawancin yankin Darfur da ke yammaci da wasu sassan kudanci.
Birnin El-Obaid dai wanda shi ne babban birnin jihar Kordofan, yana da matuƙar muhimmanci ga Khartoum, babban birnin ƙasar. Wannan ne wani yunƙuri na sojoji a ƴan makonnin nan tun bayan kame yankuna da dama na Khartoum daga hannun RSF.
Al’ummar Sudan sun fito tituna suna ta bayyana farin cikinsu dangane da sake ƙwato birnin daga hannun waɗanda suke bayyanawa a matsayin ƴan tawaye.
Wata mai fafutuka ƴar ƙasar Sudan, Dallia Abdlemoniem ta shaida wa BBC cewa ƙwace iko da birnin daga hannun RSF “gagarumar” nasara ce.
Ta ƙara da cewa sojoji na ci gaba da shirin kutsawa yammaci inda a can ne mayaƙan na RSF suke.
Dukkannin ɓangarorin biyu na sojojin gwamnati da na rundunar mayaƙan RSF sun musanta zarge-zargen take haƙƙin bil’ada da aka yi musu, da har ta kai Amurka ta ƙaƙaba wa jagororinsu takunkumai. Bugu da ƙari, an zargi RSF da aikata laifukan kisan ƙare dangi a Darfur.
An soki ƙasar Kenya bisa karɓar ɓakuncin da ta yi makon da ya wuce da ke son kafa gwamnatin ƴan aware.
Da ma dai gwamnatin sojin Sudan ta gargaɗi Kenya da cewa za ta yi ramuwar gayya kan Kenyar bisa matakin, kuma tuni ta yi wa jakadanta da ke Nairobi kiranye.
Sai dai a wani martani da suka yi, ministan harkokin wajen Kenya ya ce babu “wata mummunar manufa” a “bai wa dukkan ɓangarorin da ke rikici da juna dama.
bbc
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai5 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai5 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai7 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai19 hours agoHukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani
-
Labarai2 days agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
