Labarai
Mambobin APC Sun Kai 158,697 a Zamfara Bayan Sauya Shekar Gwamna Lawal
Adadin mambobin jam’iyyar APC a jihar Zamfara ya karu zuwa 158,697, kwanaki uku kacal bayan sake bude tsarin rajistar mambobi ta yanar gizo na jam’iyyar, biyo bayan sauya shekar Gwamna Dauda Lawal zuwa jam’iyyar.
Sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ne ya bayyana hakan yayin da yake duba yadda ake gudanar da rajistar a cibiyoyi shida da ke kananan hukumomin Gusau da Bungudu.
A wata sanarwa da Mai ba Sakataren Gwamnatin Jihar shawara kan harkokin yada labarai, Suleman Ahmad Tudu, ya fitar, an ce Malam Nakwada ya nuna gamsuwa da yadda magoya bayan gwamnan suka fito da yawa domin yin rajista a APC.
Ya ce wannan lamari alama ce da ke nuna goyon bayan jama’a ga matakin da gwamnan ya dauka na shiga jam’iyyar.
Sanarwar ta kara da cewa sabbin mambobi 60,987 ne suka yi rajista cikin kwanaki uku da sake bude shafin rajistar, baya ga 97,710 da suka riga sun yi rajista tun kafin sauya shekar gwamnan.
Hakan ya sa jimillar mambobin APC a jihar ta kai 158,697 zuwa karfe 7:30 na yammacin ranar 15 ga Maris.
Haka kuma, a matsakaici ana samun kusan mutane 20,329 na yin rajista a kowace rana, abin da jami’an jam’iyyar suka ce na nuna karuwar goyon bayan jama’a ga APC a matakin kasa.
Malam Nakwada ya bayyana fatan cewa jam’iyyar za ta cimma adadin mambobin da take bukata kafin ranar 25 ga Maris, idan aka ci gaba da samun irin wannan yawan masu rajista.
Yayin ziyararsa a Bungudu, Sakataren gwamnatin jihar ya kuma shirya wata ganawar kai tsaye ta yanar gizo tsakanin masu rajistar da Gwamna Dauda Lawal, wanda ke kasar Saudiyya domin gudanar da Umrah.
A cikin ganawar, gwamnan ya yaba wa magoya bayansa bisa juriyar da suka nuna da kuma yadda suka fito da yawa duk da tsananin zafi da kuma azumin watan Ramadan.
Ya kuma sake jaddada kudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiki domin kare muradun al’ummar jihar Zamfara.
Sakataren gwamnatin ya samu rakiyar mai kula da rajistar a jihar, Hon. Naziru Ibrahim, da kuma Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin sarauta, Injiniya Ahmad Garba Yandi, tare da sauran jami’ai.
Aminu Dalhatu/Gusau
-
Labarai6 days agoAn Nada Kabir Yahaya Darakta Janar na Farko na Filin Jirgin Sama da ke Gusau
-
Labarai5 days agoTinubu Ya Nada Lamido Yuguda Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Kasa
-
Labarai6 days agoKwastam ta Kama Kayayyaki na Sama da Naira Miliyan 478 a Jihar Kwara
-
Labarai4 days agoJami’ar Bayero Kano Ta Yi Martani Kan Zargin Damfarar Dalibi
-
Labarai4 days agoKwastam Ta Kama Kayayyakin Fasa Kwauri Na Naira Miliyan 478 A Kwara
-
Labarai4 days agoAn Yi Wa Jami’an FRSC A Jos Gwajin Idanu Kyauta Domin Ranar Glaucoma Ta Duniya
-
Labarai4 days agoMatashi Mai Digiri Na Farko Na Sayar Da Ruwan Leda A Taraba
-
Labarai1 day agoJIBWIS Ta Bukaci Gwamna Bago Ya Gaggauta Sanya Hannu Kan Dokar Hisbah
