Labarai
Manyan Alkalai Sun Bukaci Birtaniya Ta Daina Siyar wa Isra’ila Makamai
Tsofaffin alƙalan kotun ƙoli sun bi sahun masana shari’a fiye da 600 wajen kira ga gwamnatin Birtaniya ta daina sayar wa Isra’ila makamai.
Cikin wata takarda zuwa ga firaiminista Rishi Sunak, tsofaffin alƙalan sun ce dole ne a kawo ƙarshen fitar da makamai saboda Birtaniya na cikin haɗarin karya dokokin duniya.
Tuni dai mista Sunak yake fuskantar matsin lamba bayan sojojin Isra’ila sun kashe wasu ma’aikatan agaji bakwai.
A ranar Talata ne, firaiministan ya ce Birtaniya tana da wani tsari na kaffa-kaffa game da lasisin makamai.
Tsohuwar shugabar kotun ƙoli, Lady Hale na cikin masana sama da 600 da suka sa hannu kan takardar mai shafuka 17.
Takardar ta ce akwai buƙatar a ɗauki mataki na gaske domin hana Birtaniya faɗawa matsalar karya dokokin ƙasa da ƙasa har da yiwuwar saɓa yarjejeniyar da ta shafi dokokin kisan kiyashi.
Sauran mutanen da suka sa hannu kan takardar sun haɗa da tsofaffin alƙalan kotun ƙoli Lord Sumption da Lord Wilson tare da wasu alƙalai tara da manyan lauyoyi 69.
-
Fasaha6 days ago
Shugaba Tinubu Ya Kaddamar Da Kamfanin Sarrafa Sinadarin Batira a Lafiya
-
Labarai2 days ago
Jirgin Farko Na Alhazan Najeriya Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki
-
Ilimi3 days ago
Gwamnatin Jigawa Ta Bada Kwangilar Hanyar Kiyawa Zuwa Birnin Kudu
-
Labarai6 days ago
Mbappe ya sanar da cewa zai bar PSG a karshen kaka
-
Fasaha3 days ago
Kasuwar Panteka Ta Kaduna Ta Samu Lasisin Koyar Da Sana’o’i —NBTE
-
Labarai3 days ago
Sheikh Bin Uthman Ya Jaddada Muhimmancin Rikon Amana Ga Jami’an Hukumar Alhazai
-
Labarai3 days ago
Varane zai bar Manchester United
-
Labarai3 days ago
Gwamnatin Kano Ta Nada Ibrahim Garba Shugaban Tawagar ‘Yan Jarida A Hajjin Bana