Ilimi
Hukumar Kwastam Ta Wani Babban Kamu a Kano
Hukumar Kwastam ta Kano/Jigawa ta kama jimillar kafso guda 261,750 na Polyglycine (miligiram 300) da allunan Tramadol hydrochloride 228,700 (miligiram 225) da aka boye a cikin buhunan jumbo guda biyar.
Shugaban hukumar kwastam na yankin Kano, Dalhatu Abubakar, ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
Ya ce an boye magungunan ne a cikin fakiti 35 na Polyglycine da kuma allunan Tramadol 28.
Yayin da yake mika haramtattun magungunan ga wakilin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, Konturola Dalhatu Abubakar, ya ce abubuwan na da illa ga lafiya da suka hada da lalata gabobi, jaraba, da rashin natsuwa, musamman a tsakanin matasa.
Abubakar yayi gargadi game da illolin da ke tattare da shaye-shayen miyagun kwayoyi, inda ya danganta ta da tashin hankali, aikata laifuka, lalata, asarar tattalin arziki, da rashin tsaro a yankin.
Ya ce an kama wani mutum da ake zargi a wurin da kudi Naira 455,500 da nufin cin hanci, tare da wata mota kirar Nissan Pathfinder mai baƙin launi (lamba mai lamba DUT196AE).
Kwanturolan ya ce kamen ya yi daidai da sashe na 55C da na 234 na dokar hukumar kwastam ta Najeriya ta 2023, wadanda suka ba da umarnin kare lafiyar jama’a da kuma haramta mallakar kayayyakin fasa-kwauri.
Mohammad Usman Mai’aduwa kwamandan masu safarar miyagun kwayoyi NDLEA Kano, ya ce hukumarsa za ta ci gaba da gudanar da binciken da ya dace kuma wadanda aka samu da laifi za a gurfanar da su a gaban kotu.
Ya nanata kudurin hukumar na ci gaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro da nufin cimma muradun jihohin.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
