Labarai
Limamin Pangu Gari Ya Nemi Gwamnan Neja Ya Sanya Baki Kan Rikicin Fili A Yankin
An yi kira ga Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja da ya sanya baki kan rikicin fili mai fadin sama da hektar saba’in da biyar da ake zargin Hakimin Tegina da ke karamar hukumar Rafi ya kwace daga hannun mamallakinsa a Pangu Gari.
Babban Limamin Pangu Gari, Alhaji Umar Musa Danladi ne ya yi wannan kiran yayin da yake zantawa da manema labarai a Minna, inda ya bayyana cewa hakan yana da muhimmanci matuka, domin dakile rikicin da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Alhaji Umar Musa Danladi ya bayyana cewa ya gaji filin gonar ne daga mahaifinsa wanda ya rasu kusan shekaru goma da suka gabata, kuma yana da burin barin filin ga ‘ya’yansa su gada.
Babban Limamin ya bayyana cewa wata kotun Shari’a da ke yankin ta shiga tsakaninsa da wani mutum da ya gina shago a cikin filin, haka kuma ya ci nasara a wata kara da ke dauke da lamba SC/Teg/Cr_25/2024 da ya shigar kan Hakimin Tegina da wasu mutum bakwai a bara.
A cewarsa, ci gaba da cin zarafin da Hakimin Tegina, Alhaji Garba Bako ke yi masa, wani abu ne da ke nuna raina kotu, wanda ya kamata a dauki mataki cikin gaggawa domin samar da zaman lafiya mai dorewa bisa ka’idojin adalci, da gaskiya da gudanar da aiki da nagarta da gwamnatin Gwamna Mohammed Umar Bago ke tsayawa a kai.
Sai dai ya zargi Hakimin Tegina, Alhaji Garba Bako, da cewa ya bayar da wani yanki na filin gonar nasa ga wasu manoma domin su noma, tare da umartar jami’an tsaro su kama Babban Limamin Pangu Gari da duk wani dan uwansa da aka gani a filin gonar.
Alhaji Musa Umar Danladi ya kuma nemi Sarkin Kagara, Alhaji Attahiru Gunna na biyu wanda ya bayyana a matsayin masoyin zaman lafiya, da ya kara shiga tsakani a rikicin filin gonar domin ya samun abin da ya ce mallakinsa ne na hakika.
Ya kuma bukaci ‘yan uwansa su ci gaba da kasancewa cikin zaman lafiya tare da jiran amsa mai kyau da shiga tsakani daga bakin Gwamnan Jihar Neja da kuma Sarkin Kagara, wadanda ya bayyana a matsayin mutane masu gaskiya da adalci akan aikinsu.
Daga Aliyu Lawa
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
