Connect with us

Labarai

An Yi Kira Ga Manoma Da ‘Yan Kasuwa Da Su Kara Sassauci A Farashin Kayayyaki

Published

on

Galadima Muri, na Masarautar Muri, kuma Hakimin Jalingo, Alhaji Lamido Abba Tukur, ya yi kira ga manoma da ‘yan kasuwa a Taraba da su yi la’akari da halin da talakawa ke ciki, su rage farashin kayan abinci.

Ya yi wannan kiran ne a yayin cikarsa shekaru 40 akan karagar mulki a matsayin Galadima a Jalingo.

Basaraken  ya nuna damuwarsa kan yadda hauhawar farashin kayayyakin abinci a kullum ke kara ta’azzara, da kuma kalubalen tattalin arziki da talakawa ke fuskanta.

Galadiman ya yabawa gwamna Agbu Kefas kan yaki da matsalar tsaro a Taraba, inda ya bayyana ci gaban da aka samu a shekarun baya-bayan nan a matsayin abin a yaba.

Amincewa da gudanar da wannan biki na cika shekara 40 akan karagar mulki a matsayin Galadima a yau, ya biyo bayan yakin da Gwamna Kefas ya yi da wajen tabbatar da ganin an shawo kan matsalar tsaro a Taraba, tare da wanzar da zaman lafiya, ba a Jalingo kadai ba, har ma a jihar Taraba baki daya, wanda ya baiwa jama’a damar samun hanyoyin samun kudaden shiga na yau da kullum“. Inji shi.

“A matsayina na babasaranaina shiga cikin damuwa matuka a duk lokacin da jama’ata suka gaza shiga gonakinsu ko gudanar da  sana’o’insu saboda rashin tsaro. Ina son in yaba wa gwamna Agbu Kefas bisa gaggarumin yaki da rashin tsaro a Taraba, wanda sannu a hankali ana samun kwanciyar hankali a halin yanzu.

Tun da farko, shugaban taron, Alhaji Kabiru Marafa, da Lamido Bakundi, mai martaba Alhaji Kabiru Muhammad Gidado Misa, sun bayyana Galadima a matsayin basarake abin koyi, wanda ake alfahari da ayyukansa da jagororinsa.

Jamila Abba

Labarai

Labarai21 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai2 days ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai2 days ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai2 days ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara