Labarai
Gwamnatin Borno Ta Samar Da Gidaje Sama Da 400 Ga ‘Yan Gudun Hijira A Dalori
Gwamnatin Jihar Borno ta fara rabon gidaje 447 na sake tsugunar da ‘yan gudun hijira a yankin Dalori dake karamar hukumar Konduga a jihar.
Gwamna Babagana Zulum wanda ya kaddamar da atisayen, ya kuma raba kayan abinci da sauran kayayyakin masarufi ga iyalan da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu.
Ya ce an zabo wadanda suka ci gajiyar tallafin ne daga sansanin ‘yan gudun hijira da ke Kawar Maila, inda iyalai 197 suka sami gidaje, yayin da iyalai 250 daga sansanin Dalori suka amfana.
Ya ce an samar wa al’ummar da aka sake tsugunar da su asibiti da makaranta da ruwan sha.
Gwamnan ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta kuma samar da kayayyakin noma da tallafa ga ‘yan kasuwa domin ‘yan gudun hijirar da suka dawo su samu saukin ababen more rayuwa.
“Kowanne daga cikin gidajen 447, wadanda suka kunshi mutane kusan dubu biyu da dari biyar sun sami kayan abinci, da tabarmi, da barguna da tufafi.” In ji Gwamna Zulum.
Zulum ya kuma yi tsokaci kan shirin sake ginawa da kuma tsugunar da al’ummar Dalwa da Sandiya da ‘yan ta’addan Boko Haram suka raba da muhallansu a karamar hukumar Konduga.
Hakazalika, Gwamna Babagana Zulum ya kuma bayar da umarnin rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira da ba hukuma ta kafa su ba a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Ya ce ba za a ci gaba da ajiye mutane a sansanoni ba, yana mai jaddada cewa za a rufe dukkan sansanoni da ke Maiduguri kafin ranar 29 ga Mayun 2024.
“Muna so a sami kamulallun mutane a cikin al’ummoma daban-daban domin bayar da gudummawar ci gaban jihar, don haka za mu mayar da su gidajensu domin su ci gaba da gudanar da al’amuran su na yau da kullun”. Inji shi.
Gwamnan ya bayyana cewa an rufe dukkanin sansanonin ‘yan gudun hijira da gwamnati ta kafa a birnin Maiduguri da kewaye tun shekarar da ta gabata.
Daga Dauda Iliya
-
Labarai4 days ago
Jirgin Farko Na Alhazan Najeriya Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki
-
Ilimi6 days ago
Gwamnatin Jigawa Ta Bada Kwangilar Hanyar Kiyawa Zuwa Birnin Kudu
-
Fasaha6 days ago
Kasuwar Panteka Ta Kaduna Ta Samu Lasisin Koyar Da Sana’o’i —NBTE
-
Labarai6 days ago
Sheikh Bin Uthman Ya Jaddada Muhimmancin Rikon Amana Ga Jami’an Hukumar Alhazai
-
Labarai3 days ago
Majalisar Dattijan Na So A Bai Wa Kananan Hukumomi Yancin Kai
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Kano Ta Nada Ibrahim Garba Shugaban Tawagar ‘Yan Jarida A Hajjin Bana
-
Labarai5 days ago
Jamhuriyar Benin Ta Haramta Fitar Da Masara Zuwa Nijar
-
Labarai6 days ago
Varane zai bar Manchester United
Haladu Abdullahi
February 28, 2024 at 5:50 am
MUNA YABAWA GOMNA BABAGANA BISA WANNAN GAGARUMI AIKI DA YAYI