Connect with us

Kasuwanci

Sabuwar Dokar CBN: Nawa Za a Iya Cirewa a ATM da POS?

Published

on

Yanzu ƴan Najeriya za su iya cire naira 100,000 ta na’urar cire kuɗi ta ATM a rana, haka ma abin yake a ɓangaren cire kuɗi ta na’urar POS.

A ɓangaren ma’aikatu kuma, za su iya cire kuɗi har naira miliyan biyar ne a duk mako.

Wannan na ƙunshe ne a cikin sabbin tsare-tsaren da Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar bayan garambawul da ya yi kan dokokin cire kuɗi ta na’urar ATM da POS a Najeriya.

Bankin ya ce wannan sabuwar dokar za ta fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2026.

A cikin wata sanarwa da daraktan tsare-tsare na bankin, Dr Rita Sike ta fitar a ranar Talata 2 ga watan Disamba, ta ce babban bankin ya yi gyara ne a kan dokokin kuɗin da za a iya cirewa.

Amma idan mutum ya cire kuɗi sama da ƙa’idar da aka ƙayyade a mako, mutum zai biya wani adadi na kuɗin.

Ya kamata ƴan Najeriya su fahimci cewa ida suka shiga cikin banki suka cire naira 100,000, shi ma yana cikin kuɗin da suka cire a rana.

Hakan na nufin za a ƙirga shi a cikin kuɗin da mutum ya cire a makon, kamar ya cire ta ATM ko POS.

Me ya sa aka yi canjin?

Kamar yadda sanarwar ta nuna, an tsara tsohuwar dokar ce domin rage ta’ammali da tsabar kuɗi da magance matsalolin tsaro da ma daƙile sama da faɗi da kuɗaɗe da sauran abubuwan da ake tunanin ba su da sauƙi sai da tsabar kuɗi.

Sauran dokokin sun haɗa da:

Cire kuɗi mai yawa – Idan ka cire kuɗi sama da adadin da ƙayyade, za ka biya kashi uku, idan kuma ma’aikata ce za ta biya kashi biyar na kuɗin.

Amfani da takardar karɓar kuɗi a banki – Idan ka tura wani da takardar karɓar kuɗi wato ‘check’, shi ma za a ƙirga a cikin adadin kuɗin da ka cire a mako.

Yadda aka fara dokar

A watan Disamban 2022 ne babban bankin Najeriya ya sanar da cewa daga ranar 9 ga wata Janairun 2023, ɗaiɗaikun mutane ba za su cire kuɗi sama da naira 100,000 ba, ma’aikatu kuma naira 500,000.

Sannan a lokacin bankin ya ce adadin kuɗin da za a iya cirewa ta na’urar POS shi ne naira 20,000.

Haka kuma a lokacin bankin ya ƙayyade cewa ƙananan takardun kuɗi irin su naira 200 zuwa ƙasa ne za a riƙa sakawa a ATM.

Bankin ya fitar da tsare-tsaren ne bayan fitar da sababbin takardun kuɗi a Najeriya.

Idan mutum zai cire sama da adadin, zai biya kashi biyar, ma’aikatu kuma za su biya kashi 10.

A baya, kuɗin da mutum zai iya cirewa ta na’urar ATM naira 100,00 ne a mako, amma mutum naira 20,000 kawai zai iya cira a kullum, amma a POS kuma, naira 20,000 kawai za a iya cirewa.

Labarai

Ilimi15 hours ago

Dr. Builder Muhammad Uba Ya Jagoranci Rangadin Makarantu a Birnin Kudu

Daga Usman Muhammad Zaria Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dakta Builder Muhammad Uba ya bayyana ilimi a...

Labarai2 days ago

Masarautar Saminaka ta Bukaci Hadin Kai Don Dorewar Zaman Lafiya a Yankin

Daga Yusuf Zubairu Majalisar Masarautar Saminaka da ke Jihar Kaduna ta yi kira ga al’ummomin da ke Karamar Hukumar Lere...

Labarai2 days ago

Hukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Kammala Shirin Rigakafi ga Maniyyatan Bana

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta kammala tanadin katin shaidar rigakafin cututtuka ga dukkan maniyyatan aikin Hajjin shekarar...

Labarai2 days ago

NEMA ta Karbi ‘Yan Najeriya 522 da Aka Dawo da su Daga Jamhuriyar Nijar

Daga Khadijah Aliyu Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta karɓi wani rukuni na ’yan Najeriya 522 da...

Labarai2 days ago

Za mu kai hari kan gidajen jami’an Amurka da Isra’ila – Iran

Hedikwatar Khatam al-Anbiya, wacce ita ce babbar cibiyar da ke kula da daidaita ayyukan rundunonin sojin Iran, ta yi barazanar...

Labarai2 days ago

Radio Nigeria @75: Tsohon Dan Jarida Ya Yi Waiwaye Kan Tarihi Radio Nijeriya

An bayyana cikar shekaru 75 da kafuwar Radio Nigeria a matsayin wani babban mataki wajen gina ci gaban zamantakewa, tattalin...

Labarai2 days ago

Ɗaya Daga Cikin Jariran nan Biyar Ya Rasu, Huɗu Na Ci Gaba Da Jinya a Asibitin Kano

Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar ɗaya daga cikin jarirai biyar da aka haifa a Asibitin...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Sadaukar Da Albashinsa Domin Sabon Asusun Tallafi Ga Sojoji

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kafa wani asusun tallafi na musamman domin taimaka wa jami’an rundunar sojin...

Labarai2 days ago

FMC Gusau ta karɓi tallafin littattafan lafiya daga gidauniyar Sir Emeka Offor

Asibitin Kula da Lafiya na Tarayya da ke Gusau, ya karɓi tarin littattafan kiwon lafiya da mujallu daga Sir Emeka...

Labarai2 days ago

NIPHID ta gudanar da gangamin wayar da kai kan tarin fuka a Zaria, Kaduna

Cibiyar kula da lafiya dake Saye Zaria, ta gudanar da gangamin wayar da kai kan cutar tarin fuka (TB) a...

Mafi Shahara