Ilimi
Jihar Kwara Ta Jaddada Kudirin Tallafa wa Wadanda Suka Tsira Daga Cin Zarafin Jinsi
Gwamnatin Jihar Kwara ta jaddada kudirinta na ba da ingantaccen kulawa da kuma ƙarfafa matakan rigakafi ga waɗanda suka tsira daga cin zarafin jima’i da na jinsi (SGBV) a fadin jihar.
Kwamishiniyar Harkokin Mata, Hajiya Opeyemi Afolashade, ce ta bayyana haka yayin ziyarar sa ido da tantance ayyuka a Cibiyoyin Tallafawa Wadanda Aka Yi wa Cin Zarafi (SARCs) da ke Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Kwara (KWASU) a Ilorin da kuma Asibitin Kwarari ta Sobi da ke Alagbado.
Kwamishiniyar ta bayyana cewa cibiyar an kafa ne tare da hadin gwiwar ofishin Uwargidar Gwamna, domin jinya kyauta da kuma kwantar da hankali, da tallafi ga wadanda suka tsira daga cin zarafi a jihar.
Afolashade ta ƙara da cewa bincike da tantancewar da ake yi yanzu zai taimaka wajen tantance ingancin kulawar da ake bayarwa, da gano wuraren da ake bukatar gyara domin samar da tsarin taimako mai inganci da niyya kai tsaye ga masu bukata.
Ta kuma jaddada bukatar ƙara haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki tare da horar da ma’aikatan cibiyoyin SARC a fannin tattara bayanai da bayar da rahoto domin inganta tsarin tallafi ga wadanda suka tsira daga cin zarafin jinsi.
Ali Muhammad Rabiu/Ilorin
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
