Labarai
ADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
Daga Isma’il Adamu
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta ƙaddamar da yakin neman zabenta a shiyyar Daura ta Jihar Katsina, inda ta sake jaddada matsayinta na dawo da tallafin man fetur, sake buɗe iyakokin ƙasa na kasar nan da kuma yafe bashin karatu da aka ba ɗalibai, game da sauran matakan da za su rage wa ’yan ƙasa raɗaɗin matsin tattalin arziki.
Da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar a babban gangamin wanda aka gudanar a Daura, Shugaban Kwamitin Yaƙin neman Zaɓen ADC, Alhaji Surajo Aminu Makera, ya ce waɗannan manufofi za su taimaka wajen bunƙasa noma da masana’antu tare da samar da yanayi mai kyau da zai ba tattalin arzikin ƙasa damar farfaɗowa.
“Idan ADC ta karɓi ragamar gwamnati a matakin tarayya, abin da zamu fara aiyanawa shine dawo da tallafin man fetur, sake buɗe iyakokin ƙasa, da kuma aiwatar da jerin manufofi da za su rage wa ’yan ƙasar nan raɗaɗi sakamakon matsin tattalin arziki .
“Cire tallafin man fetur ya ƙara jefa harkokin noma da masana’antu cikin matsala. Ƙanana da matsakaitan masana’antu na shan wahala matuka, domin kuɗin da ya kamata su rika jujjuyawa shi suke kashewa wajen sayen man fetur, biyan haraji da kuma siyan kaya a kan farashi mai tsada.
“Wannan ba alheri ba ne ga tattalin arziki; yana shafar samar da kaya, yana haddasa rasa aiyukan yi, sannan yana ƙara talauci a tsakanin ‘yan kasa” in ji Surajo Makera.
Ya ce idan aka ba jam’iyyar ADC dama, za ta fito da wasu manufofi da sauye-sauye da za su bunƙasa tattalin arziki ta hanyar samar da ayyukan yi a ɓangaren noma da masana’antu, tare da saka hannun jari a muhimman abubuwan more rayuwa kamar wutar lantarki, fasahar sadarwa ta zamani da manyan aiyuka.

Surajo Makera, wanda wani jigo a jam’iyyar, Alh Aliyu Mohammed Kurfi, ya wakilta a wajen taron, ya jaddada muhimmancin haɗin kai, ɗa’a da kuma ci gaba da nemo magoya baya yayin ake tunkarar zaɓen 2027.
A nasa jawabin, ɗan takarar Majalisar Dattawa karkashin tutar jam’iyyar ta ADC a shiyyar Daura, Alhaji Sani Lawal Garki, ya ce jam’iyyar zata aiwatar da manufofin da za su inganta tattalin arziki da tsaro da kuma mayar da hankali kan samun walwala ga ƙasa.
Ya ce matsayar jam’iyyar kan dawo da tallafin man fetur, sake buɗe iyakokin ƙasa da kuma yafe bashin da ake ba ɗalibai na daga cikin manyan tsare-tsare na rage matsin tattalin arziki ga talakawan Najeriya ke fama da shi a halin yanzu.
Game da harkar ilimi kuwa, Sani Lawal Garki ya ce shirin jam’iyyar na yafe bashin da ake bin ɗalibai zai sauke wa daliban nauyin da ke kansu, tare da tabbatar da cewa rashin kuɗi bai zama kalubale ba ga samun damar yin karatun gaba da sakandare.
Ya ce zai kuma ba manufofin ADC kan harkar tsaro muhimmanci, musamman ganin yadda ’yan bindiga ke shiga kananan hukumomin Kankia da Kusada wadanda ke shiyyar ta Daura, lamarin da ya danganta da rashin daukar matakan da suka kamata domin magance matsalar.
A nasa jawabin, wani jigo a jam’iyyar, Alhaji Lawal Batagarawa, ya yi kira ga al’umar shiyyar Daura da su zabi mutane masu nagarta a zaben 2027, yana mai kira ga magoya bayan jam’iyyar ADC da su ƙara kaimi wajen wayar da kan jama’a domin isar da saƙon jam’iyyar ga al’ummomin da ke faɗin shiyyar.
A wajen taron an gabatar da tutoci ga ’yan takarar jam’iyyar na kujerar Dan Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai ta Tarayya da Majalisar Dokokin Jiha.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai7 days agoGwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
