Labarai
Radio Nigeria @75: Tsohon Dan Jarida Ya Yi Waiwaye Kan Tarihi Radio Nijeriya
An bayyana cikar shekaru 75 da kafuwar Radio Nigeria a matsayin wani babban mataki wajen gina ci gaban zamantakewa, tattalin arziki da al’adun ƙasar nan.
Tsohon Daraktan gudanarwa na Radio Nigeria Kaduna kuma gogaggen ɗan jarida, Alhaji Halilu Ahmad Getso, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da wakilin Radio Nigeria a Kano, a wani ɓangare na bikin cika shekaru 75 da kafuwar gidan rediyon.
Getso ya ce asalin kafuwar wannan hukuma ya samo tushe ne tun zamanin Nigerian Broadcasting Corporation (NBC), wadda aka kafa a lokacin marigayi Firimiya na Arewacin Najeriya, Ahmadu Bello.
Ya bayyana cewa a farkon shekarun, an kafa ƙananan tashoshi ne kawai a Kano da Maiduguri, waɗanda ake haɗawa da Kaduna domin watsa shirye-shirye da kuma daidaita ayyukan rediyo.
A cewarsa, gidan rediyon ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa rayuwar al’umma ta hanyar shirye-shirye masu tasiri da suka mayar da hankali kan bukatun jama’a, ilimi da kuma kyawawan ɗabi’u.
Gogaggen ɗan jaridar ya kuma tuna da yadda hukumomin tsohuwar gwamnatin yankin Arewa suka sayo rediyo tare da rarraba su ga al’ummomin karkara domin ƙara musu damar samun bayanai da sadarwa.
Ya ƙara da cewa a wancan lokaci, shahararrun shirye-shirye sun haɗa da karatun Alƙur’ani da kuma shirye-shiryen da suka shafi ci gaban al’umma, waɗanda suka ja hankalin masu sauraro da dama.
Getso ya kuma bayyana cewa yawancin ma’aikatan Hukumar Rediyon Tarayya ta Najeriya (FRCN) a yanzu, sun fara aiki ne tun a NBC, abin da ke nuna ci gaba da gogewa a cikin tsarin aikin.
Ya ce kamfanin watsa shirye-shirye na Arewacin Najeriya, wanda shi ma aka kafa a ƙarƙashin jagorancin Ahmadu Bello, daga bisani ya rikide zuwa Radio Nigeria Kaduna, lamarin da ya ƙarfafa harkar watsa shirye-shirye a yankin.
Yayin da yake yaba gudunmawar da gidan rediyon ya bayar tsawon shekaru, Getso ya buƙaci ma’aikata su ƙara ƙaimi wajen inganta ayyukan su domin su dace da sabbin ƙa’idojin aikin watsa shirye-shirye na zamani.
Haka kuma, ya yi addu’ar fatan alheri ga ci gaba da ɗaukakar Radio Nigeria da sauran tashoshin FRCN a faɗin ƙasar.
Abdullahi Jalaluddeen, Kano
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai23 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
