Labarai
Ɗaya Daga Cikin Jariran nan Biyar Ya Rasu, Huɗu Na Ci Gaba Da Jinya a Asibitin Kano
Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar ɗaya daga cikin jarirai biyar da aka haifa a Asibitin Kwararru ta Murtala Muhammad dake Kano, yayin da sauran huɗun ke ci gaba da samun kulawa ta musamman.
A cikin wata sanarwa da jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar, Samira Suleiman ta fitar, ta ce an haifi jariran ne kafin cikar wa’adin haihuwa, inda aka kwantar da su a sashen kula da jarirai masu buƙatar kulawa ta musamman, domin jinyar matsalolin ƙarancin nauyi da haihuwa da wuri da sauran matsaloli masu alaƙa da hakan.
Hukumar ta bayyana cewa nan take aka sanya dukkan jariran biyar a karkashin kulawa ta musamman, ciki har da amfani da na’urar incubator, da kuma magungunan rigakafin cututtuka, waɗanda daga bisani aka ƙara inganta su bisa ga yadda yanayin lafiyarsu ke buƙata.
Da take bayani kan halin da suke ciki, hukumar ta ce jariri na farko, mace mai nauyin kilo 1.3, ta rasu duk da an yi mata ƙarin jini, sakamakon matsalolin da suka shafi tsayawar numfashi (apnoea).
A cewar hukumar, dukkan jariran sun fuskanci matsalar saukar sukarin jini (hypoglycaemia), amma an shawo kan lamarin cikin gaggawa bisa ƙa’idojin likitanci.
Haka kuma, ta ce ana yi wa dukkan jariran hasken jinya (phototherapy) domin magance ciwon jaundice na jarirai, wanda galibi ke faruwa ga waɗanda aka haifa da wuri.
Ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar, Mansur Mudi Nagoda, HMB ta ce an ɗauki dukkan matakan jinya da suka dace tun daga lokacin haihuwa har zuwa kulawar da ake ci gaba da yi musu.
Duk da haka, hukumar ta jaddada cewa irin waɗannan haihuwar jarirai da yawa a lokaci guda kafin lokaci na da matuƙar haɗari a fannin likitanci, duk da ƙoƙarin da ake yi na ba su kulawa mafi inganci.
Hukumar ta kuma yaba da ƙwazon da jajircewar ma’aikatan lafiya na sashen haihuwa da na kula da jarirai, tana mai cewa matakan gaggawa da suka ɗauka na taka muhimmiyar rawa wajen kula da jariran da suka rage.
Khadijah Aliyu
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
