Ilimi
Gwamnatin Borno Za Ta Kashe Naira Biliyan Daya Don Horar Da Malaman Makarantu
Gwamnatin Jihar Borno ta amince da kashe naira miliyan dubu daya domin horar da malaman makarantun firamare a fadin kananan hukumomi ashirin da bakwai na jihar.
Gwamna Babagana Zulum ya amince da hakan ne a lokacin da yake kaddamar da sabbin sakatarorin ilimi na kananan hukumomi da aka nada a Maiduguri.
Ya yi nuni da cewa sama da malamai dubu daya da ke da takardar shaidar kammala karatun sakandare za su kara samun horon da zai ba su damar samun karancin cancantar koyarwa.
” Horon zai hada da malaman da ba su da kwarewar koyarwa amma an gano cewa za su iya ba da horo bisa bayanan gwajin cancantar da aka yi musu,” in ji Zulum.
Gwamnan ya bukaci sabbin sakatarorin ilimi da aka nada da su maida hankali akan aikinsu, inda ya yi gargadin cewa duk wanda aka samu da gazawa za a maye gurbinsa.
“Na umurci mai girma kwamishinan ilimi da ya ba ni rahoto kan ayyukan kowace sakatariyar ilimi. Za a maye gurbin wadanda suka kasa cimma bukatun gwamnati,” in ji Zulum.
Kwamishinan ilimi, kimiya, fasaha da kirkire-kirkire, Lawan Wakilbe, ya ce mutane 126 ne suka nemi wannan matsayi kuma bayan kammala jarrabawar tantancewa, an zabo ashirin da bakwai bisa ga kwazon da suka yi.
A halin da ake ciki, Gwamna Babagana Zulum ya bayar da motocin hamsin da takwas ga sakatarorin ilimin da jami’an sa ido a fadin kananan hukumomi ashirin da bakwai da ke jihar.
Dauda Iliya
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
