Labaran Ketare
Isra’ila ta ƙaddamar da hari kan asibitin al-Shifa a Gaza
Sojojin Isra’ila sun sanar da ƙaddamar da hari kan asibitin al-Shifa da ke Gaza.
Mai magana da yawun sojin Isra’ilar, Rear Admiral Daniel Hagari, ya ce sojoji sun gano matattarar Hamas da sake shiri ta amfani da asibitin domin kai musu hari.
Hagari ya ce “muna kira ga ‘yan ta’addar Hamas da ke ɓuya a asibitoci, su mika wuya ba tare da ɓata lokaci ba, asibitoci ba wurin aikata ta’addanci ba ne”.
Wani bidiyo da aka aike wa BBC ya nuna ɗaruruwan farar hula na ficewa daga asibitin, cikin tsananin duhu suna amfani da hasken wayar salula domin haska hanya.
Wata sanarwa daga ma’aikatar lafiyar Hamas ta kira harin a matsayin take dokar jin ƙai ta ƙasa da ƙasa”.
Ɗaruruwan Falasɗinawa da suka ɗaiɗaita ne ke samun mafaka a asibitin da sojojin Isra’ila suka kai wa samame a farkon soma yaƙin.
Al-Shifa shi ne babban asibitin Gaza kafin yaƙin amma ayyukansa sun fuskanci cikas bayan shafe watanni ana gumurzu.
-
Labarai4 days ago
Jirgin Farko Na Alhazan Najeriya Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki
-
Ilimi6 days ago
Gwamnatin Jigawa Ta Bada Kwangilar Hanyar Kiyawa Zuwa Birnin Kudu
-
Fasaha6 days ago
Kasuwar Panteka Ta Kaduna Ta Samu Lasisin Koyar Da Sana’o’i —NBTE
-
Labarai6 days ago
Sheikh Bin Uthman Ya Jaddada Muhimmancin Rikon Amana Ga Jami’an Hukumar Alhazai
-
Labarai3 days ago
Majalisar Dattijan Na So A Bai Wa Kananan Hukumomi Yancin Kai
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Kano Ta Nada Ibrahim Garba Shugaban Tawagar ‘Yan Jarida A Hajjin Bana
-
Labarai6 days ago
Varane zai bar Manchester United
-
Labarai5 days ago
Jamhuriyar Benin Ta Haramta Fitar Da Masara Zuwa Nijar