Connect with us

Fasaha

Wadanda Suka Kashe Dakarunmu Za Su Dandana Kudarsu — Shugaba Tinubu

Published

on

Shugaba Bola Tinubu ya ce wadanda suka kashe dakarun soji 16 a yankin Okuoma da ke Karamar Hukumar Ughelli a Jihar Delta, za su ɗanɗana kuɗarsu.

A ranar Alhamis ne wasu bata-gari suka yi wa wasu dakarun soji kisan gilla lokacin da suke kokarin sulhunta rikici tsakanin ƙabilar Okuama da Okoloba a Jihar Delta.

Bata-garin sun hallaka Kwamandan soji daya, Manjo biyu, Kyaftin daya, sojoji 12 da kuma wani mutum daya.

Tinubu cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, ya bayyana kisan a matsayin “jahilci” da cewa dole a hukunta wadanda suke da hannu a lamarin.

Ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalan sojojin da aka kashe tare da bayyana aniyar gwamnatinsa na hukunta wadanda ke da hannu a kisan sojojin.

Shugaban ya ce, “Wannan lamarin, ya sake nuna irin hatsarin da ma’aikatanmu da mata ke fuskanta a bakin aiki. Ina jinjina wa jarumtarsu da jajircewarsu game da kishin kasa.

“A matsayinmu na al’umma, dole ne mu ci gaba da tunawa da kuma karrama duk wadanda ke bai wa kasarmu kariya. Dakarunmu da suka mutu a yankin Okuama sun bi sahun ‘yan mazan jiya.

“Jami’an sojojinmu su ne jigon kasarmu. Duk wani hari da aka kai musu hari ne kai tsaye ga al’ummarmu. Ba za mu yarda da wannan ɗanyen aiki ba.

“Na bai wa hedikwatar tsaro da babban hafsan soji cikakken ikon gurfanar da duk wanda aka samu da hannu wajen aikata wannan laifi.

“Gwamnatina ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai mun samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kowane yanki na Najeriya.”

Labarai

Labarai15 hours ago

Gini Ya Fado Kan Mutane 11 A Kano

Wani gini ya fado kan ma’aikata suna tsaka da aikin gini a unguwar Kuntau da ke Karamar Hukumar Gwale a...

Ilimi17 hours ago

Gwamnatin Qatar Za Ta Tallafa Wa Marayu 1000 A Borno

Gwamnatin Kasar Qatar ta yi alkawarin tallafawa kimanin marayu dubu daya da rikicin Boko Haram ya rutsa da iyayensu. Jakadan...

Labarai3 days ago

Jihar Jigawa Za Ta Fara Allurar Rigakafi Da Bada Unifom Ga Alhazai

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce nan ba da dadewa ba za ta fara gudanar da allurar...

Ilimi3 days ago

Daliban Jihar Kebbi Da Ke Kasashen Waje Za Su Sami Tallafin Naira Miliyan 309

Gwamnatin jihar Kebbi, ta amince da kashe sama da Naira miliyan Dari Uku da Tara, domin biyan tallafin karatu na...

Kasuwanci3 days ago

Kwari Masu Lalata Amfanin Gona Sun Mamaye Gonakin Tumatur A Kano

Shugaban kungiyar manoma ta jihar Kano, AFAN, Abdullahi Maibreadi, ya bukaci gwamnati a dukkan matakai da su taimaka wa manoma...

Fasaha3 days ago

Shugaba Tinubu Ya Kaddamar Shirin Bada Bashin Kayyaki Ga ‘Yan Kasa

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ƙaddamar da kashin farko na tsarin karɓar bashin kaya ga ƴan ƙasar. Bayanin hakan na...

Labarai3 days ago

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Rufe Bankin UBA Kan Kin Biyan Haraji

Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS) ta raufe rassan bankin UBA kan kin biyan harajin Naira miliyan 14....

Labarai4 days ago

Mutum Biyar Sun Mutu Cikin Kwale-Kwalen ƴan Ci-Rani

Mutum biyar har da yaro sun mutu yayin da suke ƙoƙarin tsallake hanyar ruwa da ta ratsa Ingila da safiyar...

Kasuwanci4 days ago

CBN Ya Sake Karya Farashin Dala Zuwa N1,101

Babban Bankin Nigeria CBN ya sake sanar da matakin karya farashin dala daga N1,251 zuwa N1,101. CBN ya bayyana haka...

Ilimi4 days ago

Ƴan Sanda Za Su Yi Bincike Kan Makarantar Leads British

Rundunar ƴan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta ce ta aika tawagar jami’anta zuwa makarantar Leads British bayan bidiyon...

Mafi Shahara