Ilimi
Mutane fiye da dubu 200 muka ba taimakon Lauya – Barista Aliyu
An bayyana bukatar sake nazarin tsarin shari’ar kasan nan muddun ana bukatar rage cinkoson da ake da shi a gidajen gyaran hali da ke fadin kasan nan
Gwamnan Jihar Plateau Caleb Muftwang ya bayyana haka lokacin da kungiyar bada tallafin aikin lauya ta kasa ta ziyarce shi a gidan gwamnati
Ita dai wannan kungiyar da ke bada agajin aikin lauya ga marasa karfj da ake tuhuma da aikata wani laifi ta zamo gatan marasa gata a kasan nan.
Don tabbatar da wannan kirarin da ake yiwa kungiyar, ta ziyarci dukkanin gidajen gyaran hali da ke kasan nan domin tabbatar da ta tallafawa wadanda ke tsare ba su da karfin daukar lauyan da zai Kare su.
Gwamnan jihar Plateau ya fadawa masu ziyarar cewa, saboda rashin adalci da daidaito ya sa ake samun aikata laifuka, don haka yace akwai bukatar yiwa tsarin shari’ar kasan nan gyaran fuska don maganin wannan matsala.
Gwamnan Wanda ya bayyana takaicin sa ganin yadda ake samun cinkoso a gidajen gyaran Hali da ke kasan Nan, yace ana shirin samarda Karin gidan gyaran Hali a Jos ta Gabas.
Tunda farko shugaban masu ziyarar kuma shugaban kungiyar Barista Aliyu Abubakar yace kungiyar su ta nada agajin lauya ga mutane fiye da dubu 200 daga shekara ta 2021 zuwa bara 2023, don yayi Kiran samun goyon baya ga kungiyar domin su ci gaba da aikin su.
Yace manufar kungiyar su, ita ce su samarda wata kasa da za a ce an Sami daidaita tsakanin dukkanin ‘yan kasa
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Tarakta 300 Ga Manoma Daga Amurka
-
Labarai7 days ago
An Samar Da Masauki Kusa Da Harami Ga Alhazan Jihar Jigawa
-
Ilimi4 days ago
Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Gidaje A Jami’ar Tarayya Da Ke Babura
-
Labarai5 days ago
An Samar Da Sabon Tsari Da Zai Inganta Harkar Noman Rogo A Najeriya
-
Fasaha1 day ago
Kusan Malaman Makaranta Dubu 2 Ke Samun Horo a Barno
-
Kasuwanci22 hours ago
CBN Ya Bai Wa Masu POS Wa’adin Yin Rajista Da Gwamnati
-
Labarai6 days ago
An kama masu zanga-zanga 17 a jami’ar Texas
-
Fasaha1 day ago
Bankuna Za Su Fara Cirar 0.5% Daga Masu Tura Kudi Ta Intanet