Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano Ta Raba Kayan Abinci Ga Majinyata A Asibitoci

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da rabon kayan abinci ga marasa lafiya da ke kwance a asibitocin gwamnati dake fadin jihar.

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, wanda ya jagoranci rabon kayayyakin da suka hada buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 19 da na masara kilogiram 10 ga majinyata a Asibitin da ake kula da cututtuka masu yaduna da na Abubakar Imam a madadin Gwamnan, ya ce an gudanar da shirin ne da nufin bada tallafiwa marasa karfi.

Ya bayyana cewa an raba buhunan shinkafa da masara dubu hudu da dari huda da ashirin da shidda ga majinyatan da ke kwance a manyan da kananan asibitoci.

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Yusuf na ba da fifiko ga shirye-shiryen da suka shafi rayuwar al’ummar jihar kai tsaye, musamman wadanda ke fuskantar kalubalen kiwon lafiya.

Dantiye ya bayyana cewa ya ji dadin ganin farin ciki a fuskokin majinyatan da suka ci gajiyar tallafin tare da jaddada kudirin gwamnati na tallafawa marasa galihu musamman a lokacin rashin lafiya.

Mun sadaukar da kai don taimakawa a duk inda aka fi bukata”

A jawabinsa, Babban jami’in kula da cututtuka masu yaduwa, Dokta Johnson Ochibo, ya ce rabon kayan agajin ga majinyatan asibitoci ya nuna jajircewar Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen kyautata rayuwar al’ummar Kano, ya kara da cewa irin wadannan tsare-tsare na nuna yadda gwamnati ke kula da bukatun al’umma.

A yayin rabon kayayyakin tallafin, kwamishinan ya samu rakiyar babban sakataren ma’aikatar ayyuka na musamman, Sunusi Abbas.

 

Khadija Aliyu

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai13 hours ago

Gini Ya Fado Kan Mutane 11 A Kano

Wani gini ya fado kan ma’aikata suna tsaka da aikin gini a unguwar Kuntau da ke Karamar Hukumar Gwale a...

Ilimi15 hours ago

Gwamnatin Qatar Za Ta Tallafa Wa Marayu 1000 A Borno

Gwamnatin Kasar Qatar ta yi alkawarin tallafawa kimanin marayu dubu daya da rikicin Boko Haram ya rutsa da iyayensu. Jakadan...

Labarai3 days ago

Jihar Jigawa Za Ta Fara Allurar Rigakafi Da Bada Unifom Ga Alhazai

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce nan ba da dadewa ba za ta fara gudanar da allurar...

Ilimi3 days ago

Daliban Jihar Kebbi Da Ke Kasashen Waje Za Su Sami Tallafin Naira Miliyan 309

Gwamnatin jihar Kebbi, ta amince da kashe sama da Naira miliyan Dari Uku da Tara, domin biyan tallafin karatu na...

Kasuwanci3 days ago

Kwari Masu Lalata Amfanin Gona Sun Mamaye Gonakin Tumatur A Kano

Shugaban kungiyar manoma ta jihar Kano, AFAN, Abdullahi Maibreadi, ya bukaci gwamnati a dukkan matakai da su taimaka wa manoma...

Fasaha3 days ago

Shugaba Tinubu Ya Kaddamar Shirin Bada Bashin Kayyaki Ga ‘Yan Kasa

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ƙaddamar da kashin farko na tsarin karɓar bashin kaya ga ƴan ƙasar. Bayanin hakan na...

Labarai3 days ago

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Rufe Bankin UBA Kan Kin Biyan Haraji

Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS) ta raufe rassan bankin UBA kan kin biyan harajin Naira miliyan 14....

Labarai4 days ago

Mutum Biyar Sun Mutu Cikin Kwale-Kwalen ƴan Ci-Rani

Mutum biyar har da yaro sun mutu yayin da suke ƙoƙarin tsallake hanyar ruwa da ta ratsa Ingila da safiyar...

Kasuwanci4 days ago

CBN Ya Sake Karya Farashin Dala Zuwa N1,101

Babban Bankin Nigeria CBN ya sake sanar da matakin karya farashin dala daga N1,251 zuwa N1,101. CBN ya bayyana haka...

Ilimi4 days ago

Ƴan Sanda Za Su Yi Bincike Kan Makarantar Leads British

Rundunar ƴan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta ce ta aika tawagar jami’anta zuwa makarantar Leads British bayan bidiyon...

Mafi Shahara