Labarai
An Kaddamar da Yin Allurar Rigakafi ga Maniyyatan Jihar Jigawa
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ƙaddamar da aikin yi wa Maniyyata aikin Hajjin 2026 allurar rigakafi.
Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse.
A cewarsa, wannan aiki na daga cikin shirye-shiryen da ake ci gaba da yi domin gudanar da aikin Hajjin 2026, inda ya jaddada kudirin hukumar na bai wa lafiyar Alhazan jihar muhimmanci.

Ya ce, kare lafiyar Alhazan jihar wajibi ne kuma nauyi ne da ya rataya a wuyan hukumar.
“Wannan aikin allurar rigakafi yana nuna shirye-shiryenmu na ganin an gudanar da Hajjin 2026 cikin nasara. Ina kira ga dukkan Alhazai da su bayar da cikakken hadin kai tare da bin ka’idojin lafiya yayin da suke shirin wannan tafiya mai alfarma.”
“Ina kuma karfafa muku gwiwa da ku kasance masu bin doka da oda tare da yin hakuri a duk tsawon lokacin aikin Hajji. Ku tabbata kun halarci dukkan tarukan wayar da kai, domin za ku sami muhimman bayanai kan yadda ake gudanar da ibadar Hajji da kuma shawarwari masu amfani ga tafiyar da ke gabanku,” In ji Labbo.

Labbo, wanda ya zagaya wajen aikin allurar rigakafin, ya ce za a ci gaba da gudanar da aikin har zuwa lokacin tashi zuwa kasa mai tsarki.
A nasa jawabin, Daraktan Ayyuka na Hukumar, Alhaji Muhammad Garba, ya sake jaddada muhimmancin bin dukkan dokoki da ka’idojin da hukumomin ƙasar Saudiyya suka shimfida domin cimma burin da ake so.
Shi ma da yake jawabi, Shugaban Tawagar Lafiya, Dakta Abubakar Habib, ya bayyana cewa an samar da isassun alluran rigakafi, da za a yi wa dukkan Maniyyatan.

Ya bayyana muhimmancin alluran da ake yi, wadanda suka hada da na sankarau, da na shan inna, da kuma zazzabin shawara.
“Wadannan allurai wajibi ne bisa dokokin lafiya na Masarautar Saudiyya. Allurar zazzabin shawara tana aiki na tsawon shekaru goma, yayin da ta sankarau ke aiki na tsawon shekaru uku. Suna da matukar muhimmanci wajen kare lafiyar mutum da ta al’umma baki daya,” in ji Dakta Habib.
Wakilinmu ya ruwaito cewa ana gudanar da aikin allurar rigakafin a dukkan kananan hukumomi 27 na jihar.
-
Labarai4 days agoRukunin Farko na Maniyyatan Jihar Jigawa Ya Tashi Zuwa Kasar Saudiyya
-
Labarai2 days agoJihar Jigawa Ta Kammala Jigilar Alhazai Zuwa Kasa Mai Tsarki
-
Labarai4 days agoRukunin Farko na Alhazan Jihar Kebbi ya Isa Kasa Mai Tsarki
-
Kasuwanci2 days agoBOA da Majalisar Wakilai za su Samar da Injinan Noma a Dukkan Mazabu
-
Labarai5 days agoKashim Shettima Ya Kaddamar da Jirgin Farko na Maniyyatan Najeriya
-
Labarai2 days agoGwamna Bago Ya Umurci SEMA Ta Gaggawata Kai Tallafi ga Wadanda Iftila’in Guguwa ya Shafa a Mokwa da Bida
-
Ilimi2 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Yaba wa Ministar Harkokin Mata Kan Inganta Rayuwar Al’umma
-
Labarai4 days agoGwamnan Jigawa Ya Bukaci Alhazai Su Yi Addu’ar Zaman Lafiya da Ci Gaban Najeriya
