Labarai
NUJ FRCN Kaduna ta Taya Farfesa Aliyu Murnar Nada Shi Shugaban Hukumar PTDF
Kungiyar Yan Jarida reshen Radio Nijeriya Kaduna NUJ FRCN ta taya Farfesa Shuaibu Shehu Aliyu murnar nadin da aka yi masa a matsayin Babban Sakataren Zartarwa kuma Shugaba na Asusun Bunkasa Fasahar Man Fetur PTDF da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nadashi
A cikin sakon taya murna, Shugaban reshen kungiyar, Umar Adamu Sarkinfada, ya bayyana nadin a matsayin wanda ya dace, yana mai cewa ya samo asali ne daga jajircewa, kwarewa, da gudunmawar da Farfesa Aliyu ya bayar wajen ci gaban kasa tsawon shekaru.
Sarkinfada ya kuma lura cewa sabon shugaban PTDF ya kasance yana da kyakkyawar alaka da Radio Nigeria Kaduna, inda yake yawan tallafa wa ci gaban kafafen yada labarai da shirye-shiryen wayar da kan jama’a.
Ya kara da cewa, tarihin aikinsa a bangarorin hidimar jama’a, ilimi, da shugabancin cibiyoyi ya sanya shi cikin wadanda suka fi dacewa da jagorantar wannan hukuma a wannan lokaci mai muhimmanci.
FRCN Kaduna ta bayyana yakinin cewa kwarewarsa da salon jagoranci za su kara inganta ayyukan hukumar, musamman wajen bunkasa jarin dan Adam da kuma kara kwarewa a bangaren man fetur na Najeriya.
Haka kuma sun yi masa addu’ar samun nasara da tasiri a wannan sabon aiki, tare da yi masa fatan Allah ya ba shi hikima da karfi wajen sauke nauyin da aka dora masa.
Yusuf Zubairu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
