Connect with us

Labarai

NDLEA Ta Kama Mutane 6 da Ake Zargi da Tu’ammali da Miyagun Kwayoyi a Harabar BUK

Published

on

Daga Abdullahi Jalaluddeen

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), reshen Kano, ta kai samame yankin  Jami’ar Bayero Kano (BUK), inda ta kama mutane shida da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi tare da rusa wasu wuraren da ake zargin ana yin wannan haramtacciyar harka.

Mai magana da yawun hukumar a Kano, ASN Sadiq Maigatari ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.

Ya ce an gudanar da aikin ne ƙarƙashin jami’an “Operation Sharar Mafaka”, bayan samun ƙorafi daga shugabancin Jami’ar  kan yadda wasu mutane ke amfani da sassan harabar jami’ar da kewayenta wajen saye da sayar da miyagun ƙwayoyi da kuma shan su.

A yayin samamen, jami’an NDLEA sun kama mutane shida da aka bayyana a matsayin masu shiga harabar ba bisa ka’ida ba, tare da kwace wasu abubuwa da ake dangantawa da harkar miyagun ƙwayoyi, sannan aka lalata su.

Kwamandan NDLEA na Kano, CN DY Lawal, ya ce wannan aiki na nuna ƙudirin hukumar na tabbatar da tsaftataccen muhalli mai aminci ga ɗalibai, ma’aikata da mazauna yankin jami’ar.

Ya ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da wannan aiki na “Operation Sharar Mafaka” domin ganowa da tarwatsawa tare da karɓe wuraren da ake amfani da su wajen aikata laifukan miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar.

NDLEA ta kuma yaba wa shugabancin jami’ar bisa haɗin kai, tana mai cewa saurin kai rahoton ya taimaka wajen gaggauta daukar mataki mai inganci kan matsalar tsaro.

Haka kuma hukumar ta yi gargaɗi ga jama’a da su guji amfani da cibiyoyin gwamnati ko wuraren jama’a wajen harkokin miyagun ƙwayoyi, tare da kira ga jama’a da su riƙa bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen bankado sauran hanyoyin masu safarar miyagun ƙwayoyi.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara