Labarai
Gwamnan Jigawa Ya Bukaci Alhazai Su Yi Addu’ar Zaman Lafiya da Ci Gaban Najeriya
Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya buƙaci Alhazan jihar da su kasance jakadu nagari yayin zamansu a ƙasa mai tsarki.
A yayin jawabin bankwana ga Alhazan a filin jirgin sama na Nuhu Muhammadu Sunusi, Malam Umar Namadi ya bukaci Alhazan da su yi addu’o’in zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Jihar.
Ya ce a cikin shekaru uku da suka gabata Alhazan Jigawa sun nuna kyawawan dabi’u a ƙasar Saudiyya. Don haka ya buƙace su da su ci gaba da riƙe wannan kyakkyawar ɗabi’a, su kasance jakadu nagari, sannan su bi dokoki da ƙa’idojin da Masarautar Saudiyya ta gindaya.
Haka kuma ya ƙarfafa musu gwiwa da su ƙara yawaita addu’o’i domin samun zaman lafiya da zaman tare cikin jituwa a jihar da ma Najeriya baki ɗaya.
Namadi ya ƙara da cewa ya kamata Alhazan su kasance kusa da jami’ai, musamman malamai da gwamnati ta tura domin jagoranta, da wayar da su kan muhimman rukunan Hajji, domin gudanar da aikin yadda ya kamata kuma karɓaɓɓe.
Jirgin da ya ɗauki rukuni na farko na Alhazai 480 ya samu halartar Amirul Hajj na jihar, Sarkin Dutse, Hamim Nuhu Muhammadu Sunusi, tare da wasu mambobin majalisar masarauta, kwamitin harkokin addini na majalisar dokokin jihar, da kuma wasu mambobin majalisar zartarwa ta jihar da sauransu.

Wasu daga cikin Alhazan da suka zanta da Rediyon Najeriya sun yaba wa hukumar kula da alhazai ta jihar bisa gudanar da tantancewa cikin tsari, tare da kula da su yadda ya kamata a sansanin alhazai da kuma a filin jirgin sama.

-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
