Connect with us

Labarai

An Kaddamar da Yin Allurar Rigakafi ga Maniyyatan Jihar Jigawa

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ƙaddamar da aikin yi wa Maniyyata aikin Hajjin 2026 allurar rigakafi.

Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse.

A cewarsa, wannan aiki na daga cikin shirye-shiryen da ake ci gaba da yi domin gudanar da aikin Hajjin 2026, inda ya jaddada kudirin hukumar na bai wa lafiyar Alhazan jihar muhimmanci.

Ya ce, kare lafiyar Alhazan jihar wajibi ne kuma nauyi ne da ya rataya a wuyan hukumar.

Wannan aikin allurar rigakafi yana nuna shirye-shiryenmu na ganin an gudanar da Hajjin 2026 cikin nasara. Ina kira ga dukkan Alhazai da su bayar da cikakken hadin kai tare da bin ka’idojin lafiya yayin da suke shirin wannan tafiya mai alfarma.”

“Ina kuma karfafa muku gwiwa da ku kasance masu bin doka da oda tare da yin hakuri a duk tsawon lokacin aikin Hajji. Ku tabbata kun halarci dukkan tarukan wayar da kai, domin za ku sami muhimman bayanai kan yadda ake gudanar da ibadar Hajji da kuma shawarwari masu amfani ga tafiyar da ke gabanku,” In ji Labbo.

Labbo, wanda ya zagaya wajen aikin allurar rigakafin, ya ce za a ci gaba da gudanar da aikin har zuwa lokacin tashi zuwa kasa mai tsarki.

A nasa jawabin, Daraktan Ayyuka na Hukumar, Alhaji Muhammad Garba, ya sake jaddada muhimmancin bin dukkan dokoki da ka’idojin da hukumomin ƙasar Saudiyya suka shimfida domin cimma burin da ake so.

Shi ma da yake jawabi, Shugaban Tawagar Lafiya, Dakta Abubakar Habib, ya bayyana cewa an samar da isassun alluran rigakafi, da za a yi wa dukkan Maniyyatan.

Ya bayyana muhimmancin alluran da ake yi, wadanda suka hada da na sankarau, da na shan inna, da kuma zazzabin shawara.

Wadannan allurai wajibi ne bisa dokokin lafiya na Masarautar Saudiyya. Allurar zazzabin shawara tana aiki na tsawon shekaru goma, yayin da ta sankarau ke aiki na tsawon shekaru uku. Suna da matukar muhimmanci wajen kare lafiyar mutum da ta al’umma baki daya,” in ji Dakta Habib.

Wakilinmu ya ruwaito cewa ana gudanar da aikin allurar rigakafin a dukkan kananan hukumomi 27 na jihar.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara