Labarai
Tinubu ya sanya wa jami’an gwamnati takunkumin fita waje na wata uku

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sa haramcin tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje tsawon wata uku ga ministoci da shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati.
Shugaban ma’aikata a fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila ne ya sanar da umarnin cikin wata takarda da aka aikewa sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.
An bayyana ƙalubalen tattalin arzikin da ake fama da shi da buƙatar alkinta kuɗin gwamnati a matsayin dalilan da suka sa aka ƙaƙaba haramcin kan tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje.
Takardar ta ce jami’i na buƙatar amincewar shugaban ƙasa idan yana son a ɗage masa haramcin kuma dole a yi hakan mako biyu kafin lokacin tafiyar.
Matakin na zuwa ne bayan bulaguron baya-bayan nan da ofishin akanta janar na ƙasa ya yi da ta janyo cece-kuce.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
