Labarai
‘Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane A Kwara
Rundunar ‘yan sanda a jihar Kwara ta kama wasu mutane goma sha daya da ake zargi da laifin yin garkuwa da mutane, da kisan kai, da fashi da makami, da mallakar makamai ta haramtacciyar hanya.
Da yake gabatar da wanda ake zargin a hedikwatar ‘yan sanda da ke Ilorin, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Victor Olaiya ya ce an kama wadanda ake zargin ne a sassa daban-daban na jihar.
A cewar sa an samu nasarar hakan ne sakamakon jajircewa, da kuma kwazon jami’an rundunar.
Mista Olaiya dukkan mutanen su 11 sun amsa laifinsu.
Ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun jagoranci masu bincike zuwa maboyar su inda aka kwato kayayyakin da suka hada da bindigogi da layu.
Kwamishinan ya bayyana cewa za a gurfanar da duk wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Mista Olaiya ya gargadi masu aikata laifuka da su sauya halayensu ko kuma su nisanci jihar.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da hada kai da sauran jami’an tsaro domin ganin an dakile aikata laifuka a jihar.
Mista Olaiya ya yi kuma yi kira ga daukacin al’umma da su sanya ido sosai tare da kai rahoton duk wani abin da baake zargi ga hukumomin tsaro domin daukar matakin gaggawa.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Fasaha6 days ago
Shugaba Tinubu Ya Kaddamar Da Kamfanin Sarrafa Sinadarin Batira a Lafiya
-
Ilimi3 days ago
Gwamnatin Jigawa Ta Bada Kwangilar Hanyar Kiyawa Zuwa Birnin Kudu
-
Labarai2 days ago
Jirgin Farko Na Alhazan Najeriya Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki
-
Labarai6 days ago
Mbappe ya sanar da cewa zai bar PSG a karshen kaka
-
Fasaha3 days ago
Kasuwar Panteka Ta Kaduna Ta Samu Lasisin Koyar Da Sana’o’i —NBTE
-
Labarai3 days ago
Sheikh Bin Uthman Ya Jaddada Muhimmancin Rikon Amana Ga Jami’an Hukumar Alhazai
-
Labarai3 days ago
Varane zai bar Manchester United
-
Labarai3 days ago
Gwamnatin Kano Ta Nada Ibrahim Garba Shugaban Tawagar ‘Yan Jarida A Hajjin Bana