Labarai
Jihar Jigawa Ta Mayar da Rarar Kudi Sama da Naira Miliyan 50 Ga Maniyyatan Aikin Hajjin 2026
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ya zuwa yanzu ta mayar da sama da naira miliyan 50 ga maniyyatan jihar na shekarar 2026, biyo bayan rage kudin kujerar aikin Hajji da Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta sanar.
Daraktan Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.
A cewarsa, an mayar da kudaden ga maniyyatan da suka riga suka biya kudin kujerunsu ga hukumar kafin a rage farashin.
Ahmed Labbo ya ce NAHCON ta sake fasalin kudin Hajj na Yankin Arewa wanda yanzu ya kai sama da naira miliyan 7 da dubu 600 yana mai jaddada cewa mayar da kudin umarni ne daga Hukumar Alhazai ta Kasa, sakamakon gagarumin ragin da aka yi wa kujerar Hajjin shekarar 2026.
Ya jinjina wa jami’an hukumar na yankuna bisa kwazon tattara takardun zuwa Hajj da bayanan maniyyata cikin sauri.
Yayin da yake magana kan shirye-shiryen aikin Hajjin 2026, Labbo ya bayyana cewa hukumar na aiki ba dare ba rana domin tabbatar da ingantattun tsare-tsare ga tawagar jihar a ƙasar Saudiyya.
Ya kuma yi kira ga maniyyata su tabbatar sun biya kudin kujerunsu kafin ko a ranar 24 ga Disamba, 2025.
Ahmed Labbo ya bayyana godiya ga Gwamna Umar Namadi bisa goyon baya da jajircewarsa ga hukumar.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
