Connect with us

Labarai

Dakarun Isra’ila sun lakaɗa wa likitoci duka a Gaza

Published

on

Falasɗinawa ma’aikatan lafiya a Gaza sun shaida wa BBC cewa dakarun Isra’ila sun rufe musu idanu da kyallaye, an tsare su kuma an tilasta musu tuɓe kayansu, yayin da aka yi ta lakaɗa musu duka a lokacin da sojin suka kai samame asibitin da suke aiki a watan Fabrairun da ya wuce.

Ahmed Abu Sabha, wani likita ne a asibitin Nasser, ya bayyana yadda sojin Isra’ilan suka tsare shi na tsawon mako guda, aka cinna mishi karnunka kuma suka karya masa hannu.

Abin da ya faru gare shi ya zo daidai da wasu likitocin biyu waɗanda suka nemi a sakaya sunayensu saboda tsoron ɗaukar matakan ramuwar gayya a kansu.

Sun shaida wa BBC cewa an muzanta su sun dake su, sun kwara musu ruwan sanyi kuma sun sanya su tsuguno mara daɗi na tsawon lokaci.

Haka kuma sun ce an tsare su na tsawon kwanaki kafin a sake su.

BBC ta bayyana wa ma’aikatar tsaron Isra’ila zarge-zargensu, amma bata mayar da martani kai tsaye kan tambayoyin da aka yi mata ba game da abubuwan da suka ce an yi musu, haka zalika bata musanta azaftarwar ba a ɗaiɗai kunsu, amma ta musanta cutar da wani jami’in lafiya a yaƙin da take yi.

Sun ce “duk wani cin zarafi na waɗanda ake tsare da su ya saɓawa umarnin ma’aikatar tsaron ta IDF, kuma don haka an haramta hakan”.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara