Labarai
BIKIN KARAMAR SALLAH: NSCDC Ta Tura Jami’ai 3,200 a Kano.

Rundunar tsaron farin kaya ta Najeriya, reshen jihar Kano, ta kammala dukkan shirye-shiryen tsaro da suka dace domin gudanar da bukukuwan karamar Sallah lafiya a jihar.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SC Ibrahim Idris Abdullahi ya fitar, ya ce kwamandan jihar, Mohammed Lawal Falala, ya amince da tura jami’ai sama da dubu uku da dari biyu a fadin jihar.
Jami’an da aka zabo daga ofisoshi na yanki da ma’aikatun za suyi aiki a filayen Idi daban-daban, wuraren shakatawa da ke a fadin Kano.
Sanarwar ta tabbatar da an tsara tsaro tare da dakile yiwuwar karya doka da oda kafin bukukuwan Sallah da bayan bukukuwan Sallah.
Sannan hukumar ta gargadin ‘yan daba da bata gari da su nisanta kansu daga duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiyar al’umma.
Jami’an rundunar a kodayaushe suna nan a kasa kuma a shirye suke don murkushe duk wanda aka kama yana karya doka a jihar.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO/Wababe
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
