Labarai
Gwamnatin Kwara Za Ta Bunƙasa Kiwon Dabbobi
Gwamnatin jihar Kwara ta ce ta shirya ɗaukar matakan zamani domin bunƙasa harkar kiwon dabbobi tare da samar da ayyukan yi ga matasa a jihar.
Kwamishiniyar kula da bunƙasa kiwon dabbobi ta jihar, Misis Oloruntoyosi Thomas, ta bayyana haka yayin makon manema labarai na NUJ reshen wakilan kafafen yaɗa labarai a Ilorin.
Ta ce gwamnati na ƙoƙarin sauya harkar kiwon dabbobi daga tsarin gargajiya zuwa tsarin kasuwanci na zamani domin ƙara yawan kuɗaɗen shiga cikin tattalin arziki.
A cewarta, jihar na shirin kafa birnin noma na zamani tare da inganta kiwon dabbobi domin ƙara yawan madarar da ake samarwa a cikin gida maimakon dogaro da shigo da ita daga ƙasashen waje.
Sauran masu jawabi a taron sun yaba da rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaba, tare da buƙatar ’yan jarida su ci gaba da gudanar da aikinsu cikin gaskiya da adalci.
Shugaban wakilan manema labarai na jihar, Kwamared Biola Azeez, ya ce aikin jarida na ƙara fuskantar ƙalubale a wannan zamani, yana mai kira ga matasan ’yan jarida su kare martabar sana’ar tare da tabbatar da sahihancin rahotanni.
Ali Muhammad Rabi’u/Ilorin
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
