Kasuwanci
BOA da Majalisar Wakilai za su Samar da Injinan Noma a Dukkan Mazabu
Daga Salihu Tsibiri
Bankin Manoma na Kasa (BOA) zai hada gwiwa da Majalisar Wakilai ta Tarayya domin bunkasa amfani da injinan noma a dukkan mazabu 360 na tarayya a fadin kasar.
Shugaban bankin, Mista Ayo Sotinriade, ya tabbatar da hakan yayin da yake zantawa da wakilan kafafen yada labarai na Majalisar, bayan gabatar da jawabi a gaban Majalisar da ya gudana a Abuja.
Mista Ayo Sotinriade ya bayyana cewa shirin na daga cikin matakan da ake dauka domin kara yawan amfanin gona, samar da ayyukan yi, rage yunwa, da kuma magance matsalolin tsaro da ke addabar kasar.
Ya kara da cewa, idan aka aiwatar da wannan hadin gwiwa yadda ya kamata, zai zama wani muhimmin sauyi daga kananan hanyoyin noma zuwa manyan ayyukan noma na kasuwanci, wanda zai bai wa Najeriya damar zama kasa mai fitar da abinci zuwa kasashen duniya.
Manajan Daraktan ya jaddada cewa, karkashin wannan sabon tsarin noma da injina, kowanne dan majalisa zai rika bayar da kashi 60 cikin 100 na kudin sayen tarakta, wanda za a ajiye a mazabarsa domin amfanin manoma na yankin.
A cewarsa, tarakta guda na iya noma akalla hekta biyar a cikin awa guda, kuma har zuwa hekta 600 a shekara. Yana mai cewa, tarakta 2,000 a fadin kasar za su iya noma kusan hekta miliyan 1 da dubu 200 na gonaki a kowace shekara.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
