Labarai
Hukumar Alhazai ta Jihar Kano ta Mayar da Rarar Kudade ga Alhazai
Daga Abdullahi Jalaluddeen
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta kammala biyan rarar kuɗaɗe ga maniyyata aikin Hajjin 2026.
Daraktan Janar na Hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai, inda ya ce an biya kuɗaɗen ga maniyyatan da suka riga suka biya kuɗin farko na Aikin Hajji.
Ya bayyana cewa kimanin rukuni biyar na maniyyata ne suka amfana da wannan kuɗin da aka dawo musu da shi, wanda ya kasance ragowar kuɗin da suka biya ne a baya.
A cewarsa, an fara ƙayyade kuɗin Hajji a kan Naira Miliyan 8 da rabi, inda daga baya aka rage zuwa Naira Miliyan 7 da dubu 696, inda aka mayar da sauran kudin ga maniyyatan da abin ya shafa.
Matawalle ya shawarci duk wani maniyyaci da bai karɓi nasa rarar kuɗin ba da ya tuntuɓi bankinsa ko kuma jami’in Hajji na ƙaramar hukumar sa.
Ya ƙara da cewa Hukumar ta riga ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta dangane da biyan dukkan kuɗaɗen da suka yi rara.
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
