Labarai
Kebbi: An Samu Asarar Rayuka a Rikicin Alwasa
Daga Sani Dutsinma
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kebbi ta ce an dawo da zaman lafiya a ƙauyen Alwasa da ke Ƙaramar Hukumar Argungu.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, SP Bashir Usman, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.
Ya ce ƙauyen Alwasa na cikin kulawar tsaro, biyo bayan gaggauta tura jami’an ‘yan sanda tare da ƙarin dakaru, waɗanda ke kan aiki domin sa ido kan yanayin tsaro, tabbatar da doka da oda, da kuma hana sake ɓarkewar rikici.
A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne a lokacin bikin Sallah, inda rikici ya ɓarke tsakanin wasu matasa, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka, yayin da wasu suka jikkata, wadanda a halin yanzu suke samun kulawa a Asibitin Gwamnati na Argungu.
Bayan wannan, an samu harin ramuwar gayya wanda ya haifar da ƙarin asarar rayuka. Rundunar ‘yan sandan ta ce ta fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin, tare da ƙoƙarin gano da kama duk waɗanda ke da hannu a ciki.
Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, CP Umar Mohammed Hadejia, ya yi Allah-wadai da lamarin, tare da gargadin cewa duk wanda aka samu da hannu cikin aikata laifi ko tayar da tarzoma zai fuskanci fushin hukunma.
Ya kuma buƙaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, su guji yaɗa jita-jita, su kuma kauce wa ɗaukar doka a hannunsu, yana mai cewa za a ci gaba da sanar da jama’a.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
