Labarai
’Yan Sanda Sun Kama Mutane Biyu Kan Lalata Kayan Wutar Lantarki a Nasarawa
Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da lalata igiyoyi da sandunan wutar lantarki a hanyar Gitata zuwa Gunduma a karamar hukumar Keffi.
Cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Ramhan Nansel, ya fitar, ya ce an gano wadanda ake zargin da suna Chigozie Igbokwe da Emmanuel John, dukkansu mazauna Jikwoyi a Abuja.
Sanarwar ta ce an kwato wasu kayayyaki daga hannunsu da suka hada da almakashi na karfe, filaya, mabudai, igiyoyin wuta, da kuma mota kirar Hyundai Sonata mai launin toka mai lambar rajista GWA 44 PM, wadda ake zargin sun yi amfani da ita wajen daukar kayayyakin da suka lalata.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Shatima Jauro Mohammed, ya umarci a mika lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar a Lafia domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.
Aliyu Muraki/Lafia
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
