Labarai
Hadarin Jirgin Ruwa A Karamar Hukumar Borgu Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 29
An gano gawarwaki 29, yayin da aka ceto mutane 50 daga wani hadarin jirgin ruwa da ya auku a kauyen Gausawa na yankin Malale a karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.
Lamarin ya faru ne ranar Talata da misalin ƙarfe 11 da rabi na safe, lokacin da jirgin ruwan da ke ɗauke da mutane 90 ciki har da mata da yara, ya nutse.
Matafiyan sun taso ne daga Tugan Sule da ke yankin Shagunu a kan hanyarsu ta zuwa Dugga domin yin ta’aziyya.
Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, ya danganta hatsarin da ɗaukar mutane fiye da ƙima da kuma karo da tushen itace a cikin ruwa, inda ya ce har yanzu ana ci gaba da neman mutane biyu daga cikin su.
A halin yanzu dai, ana ci gaba da aikin ceto da bincike domin gano sauran mutanen da ba a same su ba.
Daga AliyuLawal
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai24 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
