Ilimi
Malaman Makarantu A Jigawa Sun Yaba Wa UNICEF Bisa Horaswar Da Suka Samu
Malamai da shugabannin makarantu daga kananan hukumomi goma na jihar Jigawa sun yaba wa Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, da Kungiyar Tarayyar Turai (EU), da Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Jigawa (SUBEB), bisa horas da malamai 402 kan koyar da yaran aji na farko ta hanyar wasa.
Wasu daga cikin mahalarta daga Kiyawa, Birnin Kudu, Kafin Hausa da Hadejia sun nuna godiya ga masu daukar nauyi da masu shirya taron, inda suka ce horaswar ta koya musu sabbin dabarun koyarwa da za su inganta darussa a aji.

A yayin taron da aka gudanar a Birnin Kudu a rana ta biyar, shugaban makarantar Zango, Malam Umar Isyaku, ya bayyana shirin a matsayin abin a yaba. Ya ce, horaswar ta sa malaman sun gane cewa hanyoyin koyarwar da suka saba ba su dace ba idan aka kwatanta da sabuwar hanya da ke karfafa yaran su koya da kansu.
Daya daga cikin mahalarta horaswar, Malama Sa’adatu Adamu daga makarantar firamare ta Kauyen Maigwaram, ta ce ta lura cewa yara, musamman a matakin farko, suna fahimta sosai ta hanyar wasanni. Ta kara da cewa wasa ba darussa kawai yake taimaka musu su koya ba, yana sa su gano sha’awarsu da hanyoyin rayuwa da za su iya bi a gaba.

Ta roki masu shirya shirin da su fadada shi domin sauran makarantu a fadin jihar Jigawa su ma su amfana, tare da jaddada cewa ilimin yara ƙanana yana bukatar hadin kai domin samun babban tasiri.
A Kiyawa, wasu daga cikin mahalarta sun bayyana taron a matsayin mai sauya rayuwa. Daya daga cikinsu, Malam Usman Abubakar, ya gode wa UNICEF, EU da SUBEB bisa sabunta basirarsu ta hanyar sabon kundin karatun Early Childhood Care and Education (ECCE).

Ya jaddada cewa a baya malaman suna tilasta wa yara dabarun koyarwa masu tsauri, wadanda ba su dace da su ba, amma sabon tsarin yana karfafa koyo da ci gaban yara.
A cibiyar horaswa ta Kafin Hausa, Malam Isa Waliyy daga makarantar firamare ta Kafin Hausa Kudu ya ce an koya musu sabon kundin karatu da kuma sabbin dabarun koyarwa. Ya bayyana cewa an gabatar musu da “lokacin da’ira” da kuma fannoni daban-daban na koyo da suka dace da yadda kwakwalwar yara ke aiki.

Haka nan, a cibiyar horaswa ta Hadejia, daya daga cikin mahalarta taron, tare da fatan aiwatar da sabbin hanyoyin a aji domin koyarwa ta zama abin jin dadi kuma mai amfani.
Radio Nigeria ya ruwaito cewa, horaswar ta kwanaki biyar na cikin shirin aiwatar da Aikin Ilimi da Karfafa Matasa da UNICEF ke yi, tare da tallafin Tarayyar Turai, da nufin kara yawan yara maza da mata da ke cin gajiyar ilimi mai inganci a jihar Jigawa.
Usman Muhammad Zaria
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
