Labarai
TCN Ta Wayar Da Kan Al’ummomin Kaduna Kan Illar Lalata Kayan Wuta Da Gini Karkashen Babbar Wayar Wuta
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya bukaci hukumomin tsaro da Sarakuna da kuma kungiyoyin matasa su dauki matakan gaggawa wajen dakile gina gine-gine a karkashin manyan layukan lantarki da kuma hana lalata kayan hasken lantarki.
Babban Manajan TCN na Yankin Kaduna, Injiniya Nasir Mansur Fada, ne ya yi wannan kira a yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar da masu ruwa da tsaki a hedikwatar TCN da ke Mando, Kaduna.
Taron ya samu halartar Sarakuna da jami’an tsaro da kungiyoyin masu zaman kansu domin bin umarnin Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta kasa domin ci gaba da kokarin da TCN kiyi na dakile mamaye filayen layin lantarki da kare dukiyoyin kasa.
Injiniya Nasir Mansur Fada ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin al’umma da hukumomin da abin ya shafa domin samun wadataccen wutan lantarki a kasan nan.
Ya bayyana cewa an girka sababbin nauran bayarda wuta wato transformers a wurare daban-daban tare da ci gaba da ayyukan fadada samarda hasken wutan da kuma gyaran cibiyoyin wuta a fadin jihar Kaduna.
Sai dai ya kuka cewa hakka ba zata cimma ruwa ba mudin al’ummomin da ke zaune a kusa da cibiyoyin wutar suka gaza sanya ido domin kare kayyakin hasken lantarkin.
A cikin wata makala da aka gabatar mai taken Illar Lalata Kayan Wuta a Kasa, Manaja Mai Kula da Layyukan Wutan na Yankin Kaduna, Injiniya Simon Innocent, ya bayyana cewa ayyukan lalata kayan lantarki na haifar da matsaloli wajen samun wuta da kuma durkusar da ci gaban tattalin arzikin kasa.
A nasa jawabin, Mataimakin Kwamandan Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC), Ahmed Isah Audu, ya ce sanarda da jami’an akan lokaci da bayanai akan barnar da ake kan yi na da matukar muhimmanci wajen dakile ayyukan lalata kayan wuta a ko’ina cikin duniya.
An kammala taron wayar da kan ne tareda tattaunawa tsakanin mahalarta taron inda suka sha alwashin tallafa wa TCN tare da hada kai domin kare kayayyakin wuta da tabbatar da tsaro da ci gaba a al’umma.
COV: Adamu Yusuf
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
