Connect with us

Labarai

Hukumar Kula da Muhalli ta Jihar Jigawa ta Kwace Gurbatattun Kayayyaki na Miliyoyin Naira

Published

on

Hukumar Kula da Muhalli ta Jihar Jigawa (JISEPA) ta yi kira ga al’umma da su ba da hadin kai wajen tabbatar da tsafta da kuma bayar da rahoton duk wani da ake sayarwa da ba bisa ka’ida ba, ko kuma cikin rashin tsafta.

Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Adamu Sabo ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

A cewarsa, wannan kira ya zama wajibi sakamakon nasarar da hukumar ta samu na kwace gurbatattun kayayyakin na sama da naira miliyan 14 a lokacin sintiri da binciken kayayyaki a fadin jihar daga watan Janairu zuwa Yuni na shekarar 2025.

Alhaji Adamu Sabo ya kara da cewa, mafi yawancin kayayyakin da aka kwace na ci ne da suka lalace, ko kuma wadanda aka adana ba bisa ka’ida ba, ko kuma suka lalace har suna barazana ga muhalli da lafiyar jama’a.

Ya bayyana cewa wann

an sintiri na tabbatar da tsafta yana cikin ayyukan hukumar domin inganta lafiyar jama’a da tabbatar da tsaron muhalli, tare da tabbatar da ka’idojin tsafta.

Sabo ya ce dukkan kayayyakin da aka kama an kaddamar da su bayan an bi dukkan matakan doka, an tantance su, sannan aka amince da lalata su bisa dokokin kiwon lafiya na jama’a.

Wannan aikin an gudanar da shi ne bisa tsarin doka kamar yadda sashe na 5(1)(2) na Dokar Kariya ta Muhalli ta Jihar Jigawa ta shekarar 2009 (wanda aka gyara), da kuma sashe na 125(1) na Dokar Tsaron Lafiyar Jama’a ta Jihar Jigawa ta shekarar 2024 suka tanada”. In ji shi.

Ya jaddada cewa, wannan mataki  rigakafi ne na kare lafiyar jama’a da tabbatar da tsaron muhalli da tsaftar Jihar Jigawa ba don kuntatawa wani ba.

Ya kara da cewa, hukumar za ta ci gaba da yin aiki tare da kungiyoyin kasuwa, ‘yan kasuwa da shugabannin al’umma domin tabbatar da cikakken bin dokokin muhalli da na lafiyar jama’a.

 

Usman Muhammad Zaria

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara