Connect with us

Labarai

Gwamna Bago Ya Ayyana Dokar Ta-Baci A Babban Asibitin Gwamnatin Da Ke Minna

Published

on

Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja ya ayyana dokar ta-baci a Asibitin Gwamnati na Minna.

Gwamnan ya ce akwai bukatar gyaran gaggawa da cikakken sauyi a asibitin da ya lalace domin inganta ayyukan kiwon lafiya.

 

Wata sanarwa da mai ba Gwamna shawara ta musamman kan harkokin jaridu, Aisha Wakaso, ta fitar, ta bayyana cewa Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin taron majalisar zartarwa ta jiha da aka saba gudanarwa a Minna, babban birnin jihar.

 

Mohammed Umar Bago ya bayyana cewa asibitin da aka gina sama da shekaru hamsin da suka gabata ya lalace matuka, kuma baya iya biyan bukatun kiwon lafiya na al’ummar jihar da ke kara yawaita, saboda haka akwai bukatar a sabunta shi domin ya dace da zamani.

 

A cewarsa, asibitin ya yi amfani fiye da kima tsawon shekaru, kuma halin da yake ciki yanzu na dakile cimma nasarar samar da ingantaccen kulawar lafiya a Minna da kewaye.

 

Saboda haka, Gwamnan ya kafa kwamitin da ya kunshi masu ba shi shawara na musamman da sauran masu ruwa da tsaki domin gudanar da cikakken bincike kan halin da asibitin ke ciki tare da kawo shawarwari masu amfani.

 

Bisa ga rahoton kwamitin, shirye-shirye na tafiya akan rushe ginin asibitin na yanzu domin fara gina sabbin sassa da dakunan kwana a matakai daban-daban.

 

Ya bayyana cewa a lokacin aikin gine-ginen, za a kai wasu muhimman sassa da ayyuka zuwa cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko da aka zaba a fadin jihar domin tabbatar da ci gaba da samun kulawa.

 

Ya kara da cewa wannan mataki wani bangare ne na shirin gwamnati na gyara bangaren kiwon lafiya baki daya a jihar Neja domin tabbatar da cewa jama’a na da damar samun ingantattun ayyukan lafiya.

 

Gwamnatimmu ta kuduri aniyar inganta rayuwar al’ummar ta, Lafiya na daga cikin manyan abubuwan da muka sa a gaba, kuma muna da niyyar tabbatar da cewa jama’a sun ji sauyin gwamnati ta fuskar inganta ayyukan lafiya,” in ji shi.

 

Gwamna Umar Bago ya tabbatar wa jama’a cewa gwamnati za ta dauki dukkan matakan da suka dace domin rage matsaloli yayin da ake wannan sauyi, tare da tabbatar da ci gaba da samun muhimman ayyukan lafiya har zuwa kammala sabbin gine-ginen.

 

Daga Aliyu Lawal 

 

 

Labarai

Labarai21 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai24 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara