Labarai
‘Yan Sanda Sun Kama Wani Kasurgumin Barowon Shanu Da Garkuwa Da Mutane A Kasuwar Shinge
Jami’an Sashen Binciken Laifuka na Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Nasarawa (SCID) sun kama wani mai garkuwa da mutane a Kasuwar Shinge da ke Lafia, bisa rahotonnin sirri da suka samu.
An samu nasarar cafke wanda ake zargin bayan shafe dogon lokaci rundunar na nemasa ruwa a jallo saboda laifuka da dama da suka hada da garkuwa da mutane da kuma satar shanu.
A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, sannan ya jagoranci jami’an tsaro zuwa maboyarsa da ke kauyen Ruwan Baka a karamar hukumar Doma, inda aka samu bindiga kirar AK-49 mai lamba 453144 tare da alburusai.
Wannan nasarar ta biyo bayan kama wata Fatima Salisu a ‘yan kwanakin baya, wadda aka tare tana jigilar makamai daga Doma zuwa Jihar Katsina domin kaiwa miyagu.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Nasarawa, CP Shattima Jauro Mohammed, ya jaddada kudirin rundunar na ci gaba da yaki da aikata laifuka tare da tabbatar da tsaro ga dukkan mazauna jihar Nasarawa.
Ya bukaci jama’a da su kasance masu lura, tare da bayar da rahoton duk wani motsi ko aikin da ba su yarda da shi ba, domin ‘yan sanda za su ci gaba da aiki tukuru don tabbatar da zaman lafiyar al’umma.
Aliyu Muraki
-
Ilimi7 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai2 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai2 days ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
