Labarai
Uwargidar Gwamnan Zamfara Ta Sake Jaddada Kudurin Dakile Tu’ammali Da Miyagun Kwayoyi A Jihar
Mai dakin Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta sake jaddada kudurin gwamnatin jihar na ganin an kawar da tu’ammali da miyagun kwayoyi a fadin jihar.
Ta bayyana hakan ne a lokacin da ta karɓi shugabannin Hukumar Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi da Hana Safarar Mutane ta Jihar Zamfara, waɗanda suka kai mata ziyarar ban girma a fadar gwamnati da ke Gusau.

Hajiya Huriyya ta bayyana shirinta na yin aiki kafada da kafada da hukumar, domin gano ingantattun hanyoyin da za su taimaka wajen yaki da shan miyagun kwayoyi a fadin jihar.
“Muna shirin zama tare domin duba hanyoyin da za mu bi wajen magance matsalolin da kuke fuskanta, domin muna da aniyar ganin Zamfara ta nisanta daga illar tu’ammali da miyagun kwayoyi In Shaa Allah.”
Uwargidar Gwamnan ta yaba da jajircewar shugabancin hukumar, tare da tabbatar da cewa ofishinta a bude yake don hadin gwiwa a kokarin inganta rayuwar al’ummar jihar.

Ta kuma taya hukumar murna bisa nasarorin da ta samu a yayin gudanar da aikinta.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi da Hana Safarar Mutane ta Jihar Zamfara, Malam Ibrahim Ishaq Anka, ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce domin bayyana ci gaban da hukumar ta samu da kuma kalubalen da take fuskanta wajen aiwatar da aikinta.
“A ranar 1 ga watan Maris na wannan shekarar, mun karɓi jimillar mutane 52 da aka kama ana kokarin safararsu. Sojojin Najeriya ne suka cafke su a tsakanin Abuja da Jihar Kogi,” inji shi.

Malam Anka ya bayyana cewa hukumar ta gudanar da gangamin wayar da kai sosai kan illolin amfani da miyagun kwayoyi.
“Mun kuma shirya zaman wayar da kai da manyan limamai a fadin kananan hukumomi bakwai kan illolin amfani da kwayoyi, amfani da su ba bisa ka’ida ba, da kuma barazanar safarar mutane.”
Malam Anka ya bayyana wasu muhimman bukatun hukumar da suka hada da cibiyar gyaran hali, motocin aiki, gidajen kwanan jami’anta, da wasu muhimman kayayyakin aiki.
Daga Aminu Dalhatu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
