Connect with us

Labarai

Jihar Jigawa Za Ta Fara Allurar Rigakafi Da Bada Unifom Ga Alhazai

Published

on

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce nan ba da dadewa ba za ta fara gudanar da allurar rigakafi tare da raba jaka da sauran kayayyaki ga maniyyatan aikin Hajjin  2024.

Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga wakilin gidan rediyon Najeriya a hedikwatar hukumar da ke Dutse, babban birnin jihar.

Ya yi bayanin cewa allurar rigakafin ga dukkan maniyyatan jihar na daga cikin sharuddan hukumar Saudiyya na bayar da biza.

A cewarsa, ana sa ran za a fara allurar rigakafi da rarraba kayayyakin a cibiyoyin bitar Alhazai da ke fadin kananan hukumomin jihar ashirin da bakwai.

Ya kara da cewa, ana ci gaba da gudanar da taron bita ga Maniyyata  a dukkan cibiyoyin da aka kebe a fadin jihar.

Ya ce, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta kammala dukkan shirye-shiryen jigilar Alhazan jihar zuwa kasa mai tsarki cikin sauki.

Ya kuma bayyana cewa hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ce ta tsara jigilar  maniyyatan jihar ta bana, inda ta bai wa  kamfanin Max Air damar jigilar Maniyyatan jihar zuwa kasar Saudiyya.

 

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai3 days ago

Majalisar Dattijan Na So A Bai Wa Kananan Hukumomi Yancin Kai

Majalisar Dattijan Najeriya ta nemi Shugaba Tinubu ya shige gaba domin nema wa kananan hukumomi ‘yanci a wajen jihohi, wanda...

Labarai3 days ago

‘Yan Ƙwadago Sun Yi Watsi Da N48,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

  Ƙungiyar Ƙwadago NLC ta yi fatali da tayin naira 48,000 da Gwamnatin Tarayya ta gabatar a matsayin mafi ƙarancin...

Labarai3 days ago

Tinubu Zai Ciyo Bashin $500m Don Sayen Mitocin Lantarki

  Majalisar Dattawa ta sahale wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ciyo bashin Dala miliyan 500 da nufin samar da mitocin...

Ilimi3 days ago

Za A Fara Daukar Masu Sakamakon Jarabawar NECO A Jami’o’in Birtaniya

  Jami’o’in kasar Birtaniya na shirin fara daukar daliban Najeriya masu shaidar jarabawar kammala sakandare ta NECO. Shugaban hukumar shirya...

Labarai4 days ago

Jirgin Farko Na Alhazan Najeriya Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki

A yau Laraba 15 ga watan Mayun 2024 ne jirgin Najeriya na farko ya tashi da Alhazan Jihar Kebbi 423...

Labarai4 days ago

Najeriya Ta Kaddamar da Shafin Intanet Don Samun Bayanai Game da Ma’adinai

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shafin intanet ranar Talata wanda zai bai wa masu zuba jari damar samun cikakkun bayanai...

Labarai5 days ago

Tsohon Lauyan Trump Ya Ce Ubangidansa Ya Ba ‘Yar Fina-finan Batsa Toshiyar Baki

Tsohon babban lauyan Donald Trump, Michael Cohen, ya aikata abinda masu gabatar da kara su ka yi ta fatan ya...

Labarai5 days ago

Kotu Ta Yankewa Wani Mutum Hukuncin Zaman Gidan Yari Na Watanni 2 Bisa Satar Doya

Kotun Majistare da ke Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja, ta yanke wa wani mutum mai suna Isah Sani hukuncin...

Labarai5 days ago

Jamhuriyar Benin Ta Haramta Fitar Da Masara Zuwa Nijar

Jamhuriyar Benin ta hana fitar da masara zuwa ƙasashen waje a daidai lokacin da farashin hatsi ya yi tashin gwauron...

Labarai5 days ago

Gwamnatin Kano Ta Nada Ibrahim Garba Shugaban Tawagar ‘Yan Jarida A Hajjin Bana

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da nadin Ibrahim Garba Shuaibu a matsayin shugaban tawagar ‘yan jaridu a aikin Hajjin 2024....

Mafi Shahara