Connect with us

Ilimi

Jihar Jigawa Ta Amince da Naira Biliyan 3.5 a Matsayin Kudaden Tallafin UBEC 2025

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da fitar da Naira Biliyan 3 a matsayin  tallafin hadin gwiwa na kowace shekara  domin inganta ilimi a matakin farko, wato UBEC 2025 Matching Grant.

A wata sanarwa da Kwamishinan  Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na Jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar ya bayyana cewa za a yi amfani da kudaden ne wajen gina sabbin azuzuwa, gyare-gyare, haka rijiyoyin burtsatse da kuma samar da kayan koyo da koyarwa ga dalibai da malamai.

Ya ce, majalisar ta kuma amince da sama da Naira Miliyan 289 domin gina sabbin ofisoshin gudanarwa da gyare-gyare a kananan hukumomi 9 na jihar.

A cewarsa, za a yi amfani da kudaden ne wajen gina ofisoshin gudanarwa a GDASS Imam Hassan Kafin Hausa, gina rukuni 8 na wuraren ba-haya a wasu makarantun IEB da aka zaɓa, da kuma ayyukan gyare-gyare a GGASS Danzomo da SAIS Hadejia.

Ya ce waɗannan matakai na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen inganta ilimi da habaka ƙwarewar ɗan adam.

Sagir Musa Ahmed ya bayyana cewa makarantun da za a yi wa ayyukan sun haɗa da GDASS Imam Hassan a Karamar Hukumar Kafin Hausa, GDASS Danzomo a Karamar Hukumar Sule Tankarkar, SSIS Hadejia a Karamar Hukumar Hadejia, da GDASS Tarubu a Karamar Hukumar Kirikasamma.

Sauran sun haɗa da GDASS Sani Ayu a Karamar Hukumar Gumel, GDASS Shuarin a Karamar Hukumar Kiyawa,
GDASS Kaugama a Karamar Hukumar Kaugama, GDASS Kwaimawa a Karamar Hukumar Dutse, da GDASS Harbo Tsohuwa a Karamar Hukumar Miga.

Kwamishinan ya ƙara da cewa majalisar ta kuma amince da kwangilar sama da Naira Biliyan 1 domin gyaran tsofaffin gine-ginen cibiyoyin kiwon lafiya 30 da aka farfaɗo da su a bara.

Game da batun haɗin gwiwa don rage talauci kuwa, Sagir ya bayyana cewa majalisar ta amince da kashe Baira Miliyan 600 domin sabunta da faɗaɗa rajistar jin daɗin jama’a ta jihar ga Hukumar Jigawa Operation Coordination Unit da Hukumar CARES ta jihar (SCCU), kasancewar hakan shi ne sharadin shiga shirin Bankin Duniya na tallafin jin daɗin jama’a da rage talauci a jihohi.

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara