Labarai
Hukumar Alhazai Ta Jihar Kwara Ta Sanar da Wa’adin Biyan Kudin Aikin Hajjin 2026
Daga Ali Muhammad Rabi’u
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kwara ta sanya ranar 1 gawatan Disamba a matsayin wa’adin karshe na biyan kudin kujerar aikin Hajji na shekarar 2026, wanda ya kai sama da naira miliyan 7 da dubu 600.
A cikin wata sanarwa, Babban Sakataren Hukumar, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam, ya jaddada cewa babu tabbaci yiwuwar karin wa’adi.
Sanarwar ta ce hukumar za ta tura kudaden Hajji ga Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) domin cika wa’adin da Hukumar Hajjin Saudiyya ta gindaya.
Haka kuma ta tabbatar da cewa fara aikin visa wato takardar izinin shiga kasar Saudiyya zai kasance a watan Fabrairu 2026, kuma duk wani jinkiri na iya hana maniyyaci samun damar zuwa aikin Hajjin na 2026.
Sanarwar ta shawarci dukkan Maniyyata da su kammala biyan kudadensu, su mika fasfonsu ga hukumar, sannan su yi allurar rigakafi, tare da gabatar da takardar shaidar lafiya daga kowanne asibitin gwamnati.
-
Ilimi6 days agoGwamnatin Tarayya Ta Yi Alkawarin Inganta Hanyoyi, Ruwa da Wutar Lantarki a Jami’ar FUD
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Amince Da Shirin Gaggawa Na Kwana 120 Domin Farfaɗo Da Ilimi
-
Labarai6 days agoTinubu: Sabbin Dokokin Haraji Za Su Kawo Wadata Yayinda Tsofaffi Suka Talauta ‘Yan Najeriya
-
Labarai7 days agoHezbollah Da Isra’ila Za Su Yi Ganawar Gaba Da Gaba A Karon Farko
-
Labarai3 days agoƘungiyar Ci gaban Al’ummar Saminaka Ta Bai Wa ‘Yan Sanda Injin Hilux Don Ƙarfafa Tsaro
-
Labarai7 days agoAn Yi wa Yara Sama da 66,000 Rigakafin Cutar Shan Inna a Tarauni
-
Kasuwanci7 days agoMajalisar Neja ta Amince da Dokar Hana Ayyukan Baban Bola a Unguwanni
-
Labarai6 days agoHarin Shanga: Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafawa Iyalan Jama’an Tsaro da Aka Kashe
