Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jigawa Za Ta Yi Wa Yara Miliyan 1.5 Rigakafin Cutar Shan Inna

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kammala shirye-shiryen yi wa  yara sama da miliyan daya da rabi ‘yan ƙasa da shekaru biyar allurar rigakafin shan inna zuwa karshen watan  Nuwamba a jihar.

Shugaban  Hukumar Kula  Lafiya a Matakin Farko ta Jihar (JSPHCDA), Dakta Shehu Sambo, ya bayyana haka a taron tattaunawa da manema labarai na yini guda da aka shirya,  tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, a Dutse, babban birnin jihar.

Dakta Sambo, wanda Mataimakin Mai wayar da kan jama’a na hukumar, Malam Nura Ado ya wakilta, ya ce ana sa ran adadin yara 1,516,244 ne za a yi wa rigakafin a wannan watan.

Ya ƙara da cewa rigakafin watan Nuwamba za a gudanar da shi ne tare da Makon Lafiyar Uwa, Jariri da Yara (MNCH), inda ake ba mata masu juna biyu kulawar lafiya.

Dakta Sambo ya roƙi goyon bayan kafafen yada labarai domin isar da sako da kuma wayar da jama’a.

A nasa jawabin, Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Mohammed Rahama Farah, ya yaba wa jihar Jigawa bisa rage yawaitar cutar ta shan inna da kashi 58 bisa dari a shekarar 2024.

Sai dai ya yi gargadin ccewahar yanzu cutar na barazana a Najeriya , domin an samu lamura 72 a jihohi 14 a shekarar 2025, don haka akwai buƙatar ƙara faɗaɗa rigakafi.

Rahama Farah ya yi kira shugabannin kananan hukumomi da su sa ido sosai kan yadda ake gudanar da aikin domin tabbatar da nasara, tare da bukar kafofin watsa labarai su ƙara wayar da kai ga iyaye.

Ya kuma yi kira da a ɗauki aikin a matsayin na kowa da kowa domin kawo ƙarshen yaduwar cutar shan inna a Jigawa da sauran jihohin ƙasar nan.

Ita ma da yake jawabi a madadin Hukumar Kula da Lafiyar Farko ta Ƙasa (NPHCDA), Hajiya Firdaus Aminu ta yaba wa jihar bisa kyawawan shirye-shirye game da shirin yaki da cutar.

Za a gudanar da rigakafin shan innan na watan Nuwamba daga 27 ga watan Nuwamba zuwa 3 ga watan Disamba, 2025.

Aikin, tare da makon MNCH, za su gudana ne ta hanyar ƙungiyoyi 2,015 na ma’aikatan wucin-gadi a fadin kananan hukumomi 27 na jihar.

Labarai

Labarai16 hours ago

Tinubu Ya Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur

Daga Bello Wakili  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar dattijo, ɗan kasuwa kuma tsohon Gwamnan tsohuwar...

Labarai24 hours ago

Hukumar Alhazai ta Jigawa Ta Nemi Karin Kujerun Hajji na 2027

Jigawa, HuUsman Muhammad Zaria  Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta nemi karin kujerun aikin Hajjin 2027 daga Hukumar...

Labarai3 months ago

Kungiyar Zabi Sonka Reshen Kaduna Ta Kaddamar Da Kalandar Shekara

A kokarin ganin an kara karfafa dankon zumunci a tsakanin al’ummar tarayyar Najeriya da kuma jama’ar wadansu kasashe kungiyar Zabi...

Labarai3 months ago

Gwamna Namadi Ya Taya Najeriya Murnar Ranar Dimokuraɗiyya

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya taya al’ummar Najeriya da mazauna jihar murnar Ranar Dimokuraɗiyya...

Labarai3 months ago

EU Ta Ƙara Azama Wajen Tallafa Wa Arewacin Najeriya

Wata babbar tawaga ta shugabannin ofisoshin ƙasashen Tarayyar Turai (EU) da mataimakansu ƙarƙashin jagorancin Jakadan EU a Najeriya da ECOWAS,...

Labarai3 months ago

Kano: CDA Ta Raba Tan 2.85 Na Ingantattun Iri

Daga Khadijah Aliyu  Cibiyar bincike kan inganta noma a yankunan da ke da ƙarancin ruwa ta Jami’ar Bayero Kano(CDA), ta...

Labarai3 months ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 835 Don Sayen Kayan Agajin Gaggawa Saboda Ambaliya

Daga Usman Muhammad Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sayen kayayyakin agajin gaggawa na shirin tunkarar ambaliya da mayar da...

Labarai3 months ago

Jami’an Tsaro Sun yi Nasarar Hallaka ‘Yan Bindiga 6 a Zamfara

Daga Aminu Dalhatu Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Zamfara tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun yi nasarar dakile...

Labarai3 months ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince da Ƙarin Ayyuka Kan Ginin Hedikwatar Injinan Noma

Daga Usman Muhammad Zaria Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da ƙarin ayyuka na ginin hedikwatar Kamfanin Injinan Noma...

Kasuwanci3 months ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince da Sakin Kuɗaɗe Domin Gudanar da Taron Zuba Jari na 2026

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce ta amince da sakin kuɗaɗen da aka riga aka ware wa...

Mafi Shahara