Connect with us

Labarai

GMBNI Ta Yi Allah-wadai Da Kisan Gillar Wani Almajiri A Jihar Jigawa

Published

on

Wata kungiya mai suna Grassroots Mobilizers for Better Nigeria Initiative (GMBNI), ta yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi wa wani  Almajiri a ƙaramar hukumar Gwaram, Jihar Jigawa.

Ƙungiyar ta bayyana matuƙar bakin ciki da ɓacin rai game da wannan cin zarafin da aka yi wa yaron, wanda ya kai ga mutuwarsa cikin mawuyacin hali.

A cewar jami’in yankin Arewa maso Yamma na kungiyar ta GMBNI, Abbas Rufa’i Wangara, rahotanni sun nuna cewa wani Malamin makarantar Allo ya yi wa yaron bulala da har ta kai ga mutuwarsa.

Lamarin ya ƙara muni  inda ake zargin Malamin ya yanke kan gawar  yaron, ya cire mazakutarsa gabansa na sirri, sannan ya binne gawar a wani ƙaramar rami.

GMBNI ta bayyana wannan aika-aika a matsayin cin zarafin ɗan Adam.

Ƙungiyar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan mamacin, tana mai jaddada cewa babu wani yaro da ya kamata ya fuskanci irin wannan zalunci, musamman a wurin da ake koyar da ilimi da tarbiyya.

GMBNI ta nanata buƙatar gaggawar yin gyara a tsarin ilimin Almajiranci, wanda ya daɗe yana fama da sakaci, cin zarafi, da rashin kulawa.

Ta yi kira ga hukumomi a dukkan matakai da su ɗauki matakan da suka dace don kare Almajirai tare da tabbatar da sun sami ingantaccen ilimi cikin kyakkyawar kulawa.

Ƙungiyar ta kuma bukaci hukumomin tsaro da na shari’a da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin, tare da tabbatar da cewa an hukunta wanda ya aikata wannan danyen aiki ba tare da ɓata lokaci ba.

Shugabar GMBNI, Ambasada (Dr.) Fatima Mohammed Goni, ta sake jaddada aniyar ƙungiyar na kare haƙƙin yaran da ke cikin mawuyacin hali.

Ta yi kira ga ƙungiyoyin farar hula, ‘yan kasa da al’ummar duniya baki ɗaya da su haɗa kai wajen neman adalci ga mamacin da kuma tashi tsaye wajen tabbatar da  adalci da daidaito ga dukkan yara a Najeriya.

Usman Mohammed Zaria

 

Labarai

Labarai24 hours ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai2 days ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai2 days ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai2 days ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai2 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai3 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai3 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Labarai4 days ago

Yankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari

Daga Isma’il Adamu  An bayyana yakin neman zaben jam’iyyar APC a yankin Sanatan Funtua na Jihar Katsina a matsayin nasara,...

Labarai4 days ago

Namadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce an haɗa kwamitocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa...

Mafi Shahara