Labarai
An Bukaci Shugaban Kasa Ya Sa Ido Ga Aikin Biyan Kudaden Fansho

An bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya tabbatar da sa ido sosai kan yadda aka fitar da kudade naira biliyan 758 domin warware duk wasu basussukan fensho da ake bin su domin hana yin zagon kasa.
A cikin wata sanarwa da kungiyar Muslim Media Watch Group ta fitar, kodineta na kasa, Alhaji Ibrahim Abdullahi ya kuma yabawa shugaba Tinubu kan matakin da ya dauka na ragewa ‘yan fansho na tarayya daga halin kuncin da suke ciki.
A cewar sanarwar, dole ne a sanya ido sosai kan sabuwar manufar domin hana duk wani zagon kasa daga wasu Ma’aikatan Asusun Fansho (PFA) da ake zargi da batawa wasu ‘yan fansho da suka yi rajista da su rai.
Ya bayyana cewa wasu Ma’aikatan Asusun Fansho sun kara wa ‘yan fansho matsalolin da suke fuskanta ta hanyar jinkirta biyan su fansho kusan shekaru 2 bayan sun yi ritaya.
Ta ce duk irin wadannan laifuffuka da rashin iya aiki sun karfafa cin hanci da rashawa a sassan al’umma na tattalin arzikin kasa.
Sanarwar ta yi kira da a samar da cikakken tsari da ingantaccen tsarin sa ido daga fadar shugaban kasa da hukumar fansho ta kasa PENCOM wajen magance matsalolin ‘yan fansho gaba daya.
Tana kira ga Gwamnonin Jihohi a fadin Tarayya da su yi koyi da Gwamnatin Tarayya wajen biyan basussukan da ake bin Jihohi da Kananan Hukumomi.
Sanarwar ta kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta yin la’akari da yin kwaskwarima ga dokokin gudanar da shari’ar laifuka (ACJ) domin hukunta laifukan tattalin arziki da ake tafkawa a Najeriya.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Labarai4 days ago
Al’ummar Babura Sun Karrama Sabon Shugaban Asibitin Koyarwa Na Rasheed Shekoni
-
Labarai6 days ago
Gwamna Namadi Ya Bada Aikin hanyoyi 47 masu nisan kilomita 800 a sassan jihar.
-
Ilimi5 days ago
Tsangayar Ilimi Ta BUK Ta Yi Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafuwa
-
Ilimi3 days ago
An Fara Bada Horo Ga Masu Horas da Maniyatan Bana A Jigawa
-
Kasuwanci2 days ago
Hukumar NSCDC ta tura jami’an tsaro 415 domin aikin Easter a Zamfara.
-
Labarai4 days ago
KADGIS Za Ta Yi Amfani Da Sabuwar Manhajar Biyan Diyyar Filaye A Kaduna
-
Labarai7 days ago
Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa
-
Labarai3 days ago
Hukumar Alhazai ta Jigawa Ta Shirya Bitar Ga Malaman Bita na Kananan Hukumomi 27