Labarai
Uwargidan Gwamnan Jihar Kaduna Ta Raba Abinci, Tufafi Ga Marayu, Mabukata Da Malamai

Uwargidan Gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Uba Sani, ta raba kayan abinci da tufafi ga marayu, mabukata da malamai a Hayin Na’iya dake Kaduna.
An gudanar da taron ne a makarantar Ummul Muminina Hafsat Islamic Academy da ke Hayin Na’iya, Kaduna.
Hajiya Hafsat Uba Sani, wacce Hajiya Aisha Idris Maman ‘Yan Uku ta wakilta, ta jaddada bukatar ganin masu hali su tallafa wa talakawa da mabukata a cikin al’ummarsu.
“Uwargidan gwamnan ta yi imanin cewa marayu da mabukata suna bukatar soyayya, kulawa da tallafi kamar kowane yaro,” in ji ta.
“Wannan shiri ba wai kawai don samar da abinci da tufafi ba ne; yana nufin nuna musu cewa ana kaunarsu kuma ba a manta da su ba.”
“Muna karfafa gwiwar kowa da kowa da ke da hali da ya tallafa wa masu bukata,” ta kara da cewa.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban makarantar, Malam Hassan Abubakar, ya nuna matukar godiya ga uwargidan gwamnan, Hajiya Hafsat Uba Sani, saboda ci gaba da tallafinta.
Ya bayyana cewa wannan shi ne karo na biyu da take rabon kayan abinci da tufafi ga marayu, mabukata da malamai a makarantar, baya ga hidimar da take yi wa marayu fiye da shekaru goma.
“Fiye da shekaru goma, Uwargidan gwamnan tana daukar dawainiyar marayu, tana samar musu da bukatun rayuwa ba wai abinci da tufafi kawai ba. Wannan shi ne karo na biyu tana kawo wannan tallafi zuwa makarantar mu, kuma ba za mu gaji da gode mata ba,” in ji shi.
“Muna addu’a Allah ya ba ta lafiya da kuma ci gaba, Ya sa mata albarka a cikin ayyukanta,” ya kara da cewa.
Haka nan, shugabar dalibai, Malama Fatima Abdullahi, da daya daga cikin marayun da suka amfana, sun nuna godiyarsu, suna bayyana Hajiya Hafsat a matsayin uwa gare su duka.
Sun yi addu’a Allah ya ci gaba da sa ka mata da alkhairi da kareta.
A yayin taron, an rabawa wadanda suka amfana kayan abinci, zannuwan atamfa da shadda don su more bikin Sallah cikin jin dadi da walwala.
Ci gaba da kokarin jin-kai da Hajiya Hafsat Uba Sani ke yi ya sa ta sami yabo daga jama’a, yana kara tabbatar da jajircewarta wajen inganta rayuwar mabukata a Jihar Kaduna.
COV: Khadija Kubau
-
Labarai4 days ago
Al’ummar Babura Sun Karrama Sabon Shugaban Asibitin Koyarwa Na Rasheed Shekoni
-
Labarai6 days ago
Gwamna Namadi Ya Bada Aikin hanyoyi 47 masu nisan kilomita 800 a sassan jihar.
-
Ilimi5 days ago
Tsangayar Ilimi Ta BUK Ta Yi Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafuwa
-
Ilimi3 days ago
An Fara Bada Horo Ga Masu Horas da Maniyatan Bana A Jigawa
-
Kasuwanci2 days ago
Hukumar NSCDC ta tura jami’an tsaro 415 domin aikin Easter a Zamfara.
-
Labarai4 days ago
KADGIS Za Ta Yi Amfani Da Sabuwar Manhajar Biyan Diyyar Filaye A Kaduna
-
Labarai7 days ago
Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa
-
Labarai3 days ago
Hukumar Alhazai ta Jigawa Ta Shirya Bitar Ga Malaman Bita na Kananan Hukumomi 27