Ilimi
Abin Da Ya Sa Ba A Cika Satar Ɗalibai Ba A Borno — Zulum
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana riko da tsarin nan na “safe school initiative” a matsayin sirrin da ya sa ba cika samun labarin satar ‘yan makaranta ba a jihar.
Tsarin na “safe school initiative” dai wani shiri ne da ya wajabta gina katanga da daukar ma’aikata masu ɗauke da makamai domin kare lafiya da dukiya a makarantu.
Zulum ya bayyana ne Fadar Gwamnatin Najeriya jim kaɗan bayan fitowarsa daga wani taro na shuwagabanni a kasar nan.
Zulum ya ce “Mun kai akalla shekara bakwai zuwa takwas da ƙaddamar da tsarin ‘Safe School Initiative ’ a Jihar Borno.“Kusan duk makarantunmu na da katanga, mun gayyaci sojoji da ’yan sanda aikin tsare ɗalibai da makarantunmu.”
Zulum ya kara da cewa “Mun ɗauki ’yan banga da ’yan sa-kai suna taimaka wa jami’an tsaron kasar nan yadda ya kamata wurin tabbatar da tsaro a makarantun Jihar Borno.”
Gwamna Zulum ya jinjina wa jami’an tsaron bisa ƙoƙarin da ya ce suna yi wurin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Borno da sauran sassan kasar nan.
Jihar Borno dai ɗaya ce daga cikin jihohin da suka sha fama da bala’in ta’addancin kungiyar Boko Haram da ISIS masu tada ƙayar baya.
-
Labarai1 day ago
NAHCON Ta Jinjinawa Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Bisa Shirye-shiryen Hajjin Bana
-
Labarai1 day ago
Amurka Ta Dakatar Da Kudurin Kai Jirgin Bama-Bamai Zuwa Isra’ila
-
Ilimi5 days ago
Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Gidaje A Jami’ar Tarayya Da Ke Babura
-
Labarai6 days ago
An Samar Da Sabon Tsari Da Zai Inganta Harkar Noman Rogo A Najeriya
-
Fasaha2 days ago
Kusan Malaman Makaranta Dubu 2 Ke Samun Horo a Barno
-
Kasuwanci2 days ago
CBN Ya Bai Wa Masu POS Wa’adin Yin Rajista Da Gwamnati
-
Fasaha2 days ago
Bankuna Za Su Fara Cirar 0.5% Daga Masu Tura Kudi Ta Intanet
-
Labarai2 days ago
An kashe Falasɗinawa 34,800 tun fara yaƙi – Ma’aikatar lafiyar Hamas