Labarai
An umarci ma’aikatan gwamnati su rinƙa motsa jiki duk mako a Uganda

Gwamnatin Uganda ta umarci dukkan ma’aikatanta da su rinƙa ware sa’a biyu a duk mako suna motsa jiki domin su kasance cikin ƙoshin lafiya.
Gwamnatin ta ce an bayar da umarnin ne domin ceton rayukan ma’aikatan da kuma rage musu kamuwa da wasu cutuka da suka jiɓanci rashin motsa jiki.
Cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, gwamnatin ta ce an ɗauki wannan matakin ne domin a canja yanayin tsarin rayuwar ma’aikata da kuma rage haɗarin kamuwa da cutuka a ƙasar.
Gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne bayan wani bincike da hukumar lafiya ta ƙasar ta gudanar wanda ya nuna an samu ƙaruwar masu ƙiba sosai a ƙasar da ya kai daga kashi 17 cikin 100 zuwa 26 cikin 100.
Ba wannan ne karon farko da gwamnatin ta Uganda ta fara bayar da irin wannan umarni ba,ko a 2018 ma an yi wasu abubuwa makamantan haka.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
