Connect with us

Labarai

Majalisar Dattawa ta Amince da Hukuncin Kisa ga Masu Safarar Kwaya

Published

on

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da ƙudurin dokar hukuncin kisa ga masu safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasar, bayan ƙudurin ya tsallake karatu na uku a zauren majalisar.

Majalisar ta amince da ƙudurin bayan kwamitin majalisar kan ayyukan yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi, ƙarƙashin jagorancin Sanata Tahir Munguno ya gabatar da rahotonsa kan sabuwar dokar a zauren majalisar.

Yayin da take sake nazarin dokar, majalisar ta amince da dokar hukuncin kisan ne domin ƙarfafa ayyukan hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasar.

A lokacin muhawarar, babban mai tsawatarwa na majalisar, Sanata Peter Nwebonyi ya nemi majalisar ta amince da dokar hukuncin kisa ga masu safarar miyagun ƙwayoyin, maimakon ɗaurin rai -da-rai.

A lokacin da aka nemi ra’ayin sauran ‘yan majalisar dangane da batun, majalisar ta nuna amincewarta kan dokar ciki har da mataimakin shugaban majalisar dattawan ƙasar.

To sai dai wasu tsirarun ‘yan majalisar ba su goyi bayan ƙudurin ba, inda Sanata Adams Oshimole ya kasance cikin masu nuna adawa da dokar.

To sai dai mataimakin shugaban majalisar dattawan, Sanata Barau Jibril ya yi watsi da buƙatar sanata Oshimolen, yana mai cewa ƙorafin sanatan ya saɓa wa dokar majalisar saboda ƙorafin ya zo ne bayan majalisar ta amince da ƙudurin.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Fasaha19 mins ago

Shugaban Kasa Ya Kaddamar Sabon Birnin Kasuwanci A Abuja

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da samarda wani da za a samar don gudanarda harkokin kasuwanci a cikinsa da...

Labarai50 mins ago

Kungiyar CAN Ta Rasa Mata Shida A Hadarin Mota A Taraba

An bayyana cewa wasu ’yan kungiyar mata ta kungiyar Kiristoci ta Najeriya (WOWICAN) su shida ne suka rasa rayukansu a...

Labarai1 hour ago

‘Yan Sakai Jihar Taraba Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa

Rundunar ‘yan banga ta Najeriya (VGN) reshen jihar Taraba ta yi nasarar ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa...

Ilimi1 hour ago

Talatar Nan Jirgin farko na Maniyatan jihar Kwara Zai Tashi

An dage tashin jirgin farko daga filin jirgin sama na Janar Tunde Idiagbon na kasa da kasa na Ilorin don...

Labarai1 hour ago

HARIN MASALLACIN KANO: Obi Ya Ziyarci Wadanda suka Mutu

  Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LP) a zaben 2023, Peter Obi, ya ziyarci wadanda kona masallacin Kano...

Labarai2 hours ago

Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi Ta Yi Kiran A Yiwa Mijinta Addu’a

Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Zainab Nasir Idris, ta ce addu’a ita ce ginshikin duk wani shugabanci mai nasara, don...

Labarai2 hours ago

Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitin Kwanar Ganduje A Kano

Gwamnatin jihar Kano, ta rufe tare asibitin Kwanar Ganduje dake unguwar Sharada Karamar Hukumar Kano Municipal.   Babban daraktan hukumar...

Labarai2 hours ago

Shugaban Iran Ebrahim Raisi Ya Rasu A Hatsarin Jirgi

Jami’an Iran sun ce Shugaba Ebrahim Raisi da ministan harkokin wajen ƙasar, Hossein Amir-Abdollahian sun rasu a wani hatsarin jirgin...

Labarai13 hours ago

Ma’aikatan Ceto Na Cigaba Da Neman Jirgin Shugaban Kasar Iran Da Ya Bace

Da yammacin yau lahadi ne tarin ma’aikatan ceto suka bazama wajen aiki gano jirgi mai saukar ungulu dauke da shugaba...

Labarai4 days ago

Majalisar Dattijan Na So A Bai Wa Kananan Hukumomi Yancin Kai

Majalisar Dattijan Najeriya ta nemi Shugaba Tinubu ya shige gaba domin nema wa kananan hukumomi ‘yanci a wajen jihohi, wanda...

Mafi Shahara