Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria 

Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa, NAHCON, domin tabbatar da gudanar da aikin Hajjin 2027 cikin nasara.

Mataimakin Gwamnan Jihar, Injiniya Aminu Usman, ya bayyana haka  lokacin da ya karɓi tawagar NAHCON da ta kai ziyarar ban-girma Dutse, babban birnin jihar.

Ya ce gwamnati na ci gaba da ba da muhimmanci ga jin daɗin mahajjata, yana mai cewa ƙoƙarin jihar wajen gudanar da aikin Hajji ya sanya ta kasance cikin jihohin da ke kan gaba a ƙasa.

Injiniya Aminu Usman ya tabbatar wa tawagar cewa jihar za ta ci gaba da riƙe wannan matsayi, tare da yabawa NAHCON bisa ƙoƙarinta na inganta ayyukan Hajji.

Tun da farko, Kwamishinan NAHCON mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, Sheikh Muhammad Bin Uthman, ya bayyana wasu sabbin manufofin hukumar, ciki har da wajabcin duba lafiyar maniyyata aikin Hajji.

Ya jaddada muhimmancin ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin jin daɗin mahajjata na jihohi da NAHCON, domin tabbatar da ingantaccen tsari da nasarar aikin Hajji.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa tawagar ta ziyarci Jihar Jigawa ne domin tantance matakin shirye-shiryen jihar na aikin Hajjin 2027.

Shugaban Hukumar Jin Daɗin Mahajjata ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya karɓi tawagar, tare da zagayawa da ita wuraren da jihar ke amfani da su wajen gudanar da aikin Hajji.

 

Alhaji Labbo ya ce jihar a shirye take tsaf don aikin Hajjin 2027, inda ya ƙara da cewa an sayar da dukkan kujerun Hajjin da aka ware wa jihar ga maniyyata. Yana mai cewa, jihar ta  nemi ƙarin kujeru a hukumance domin biyan buƙatar da ke ƙaruwa daga masu niyyar zuwa aikin Hajji.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara